Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Yahaya - Yahaya 8

Yahaya 8:48-55

Help us?
Click on verse(s) to share them!
48Yahudawa suka amsa suka ce masa, “Bamu fadi gaskiya ba da muka ce kai Basamariye ne kuma kana da aljan?”
49Yesu ya amsa, “Ni ba ni da aljan, ina girmama Ubana, ku kuma ba kwa girmama ni.”
50Ba na neman daraja domin kaina, akwai wanda ke nema yana kuma hukuntawa.
51Hakika, hakika, iIna ce maku, dukan wanda ya kiyaye maganata, ba za ya ga mutuwa ba.”
52Sai Yahudawa su ka ce masa, Yanzu mun sani kana da aljan. Ibrahim da annabawa sun mutu, amma kai ka ce, 'dukan wanda ya yi biyayya da maganata ba zai dandana mutuwa ba'.
53Ai baka fi ubanmu Ibrahim girma ba wanda ya mutu, ko ka fi shi? Annabawa kuma sun mutu. Wa kake daukar kanka ne?”
54Yesu ya amsa, “Idan na daukaka kaina, daukaka ta banza ce, Ubana ne ya daukaka ni. Wanda kuka ce shi ne Allahnku.
55Ku kuwa ba ku san shi ba, amma ni na san shi. Idan na ce ban san shi ba, na zama kamar ku kenan, makaryaci. Sai dai, Ni na san shi ina kiyaye maganarsa.

Read Yahaya 8Yahaya 8
Compare Yahaya 8:48-55Yahaya 8:48-55