Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Yahaya - Yahaya 8

Yahaya 8:40-51

Help us?
Click on verse(s) to share them!
40Amma, yanzu kuna so ku kashe ni, mutumin da ya gaya maku gaskiyar da ya ji daga wurin Allah. Ibrahim bai yi haka ba.
41Kuna yin ayyukan ubanku. Suka ce masa, “mu ba a haife mu cikin fasikanci ba, muna da Uba daya: Allah.”
42Yesu ya ce masu, “Inda Allah Ubanku ne, da kun kaunace ni, gama na zo daga wurin Allah kuma ga ni anan, gama ba domin kaina nazo ba, shine ya aiko ni.
43Meyasa baku gane magana ta ba? Ai saboda ba za ku iya jin maganata ba ne.
44Ku na ubanku, shaidan ne, kuma kuna so ku yi nufe-nufe na ubanku. Shi mai kisan kai ne tun daga farko kuma ba ya tsayawa gaskiya saboda da babu gaskiya a cikin sa. Sa'anda yake fadin karya, yana maganar halinsa ne domin shi dama makaryaci ne da uban karya kuma.
45Dayake ina fadin gaskiya baku bada gaskiya gare ni ba.
46Wanene a cikin ku ya kama ni da zunubi? Idan na fadi gaskiya don me ba ku gaskanta ni ba?
47Shi wanda yake na Allah ya kan ji maganar Allah, ku ba kwa jin maganar Allah da yake ku ba na Allah bane,”
48Yahudawa suka amsa suka ce masa, “Bamu fadi gaskiya ba da muka ce kai Basamariye ne kuma kana da aljan?”
49Yesu ya amsa, “Ni ba ni da aljan, ina girmama Ubana, ku kuma ba kwa girmama ni.”
50Ba na neman daraja domin kaina, akwai wanda ke nema yana kuma hukuntawa.
51Hakika, hakika, iIna ce maku, dukan wanda ya kiyaye maganata, ba za ya ga mutuwa ba.”

Read Yahaya 8Yahaya 8
Compare Yahaya 8:40-51Yahaya 8:40-51