Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Yahaya - Yahaya 8

Yahaya 8:22-37

Help us?
Click on verse(s) to share them!
22Yahudawa su ka ce, “Zai kashe kansa ne, da ya ce inda ni ke tafiya ba za ku iya zuwa ba?”
23Yesu ya ce masu ku daga kasa kuke, Ni kuwa daga bisa ni ke. Ku na wannan duniya ne, Ni kuwa ba na wannan duniya ba ne.
24Shiyasa na ce maku za ku mutu cikin zunubanku. In ba kun bada gaskiya NI NE ba, za ku mutu cikin zunubanku.
25Sai kuma suka ce da shi, “Wanene kai?” Yesu ya ce masu, “Abin da na gaya maku tun daga farko.
26Ina da a bubuwa da yawa da zan gaya maku, in kuma hukunta ku a kai. Duk da haka, wanda ya aiko ni, mai gaskiya ne, abubuwan da naji daga wurin sa, wadannan abubuwan su ni ke gaya wa duniya.”
27Ba su gane ba yana yi masu magana a kan Uban.
28Yesu ya ce, “Sa'adda kuka tada Dan Mutum sama sa'annan za ku gane NI NE, kuma ban yi komi domin kaina ba. Kamar yadda Uba ya koya mani, haka nike fadin wadannan abubuwa.
29Shi wanda ya aiko ni, yana tare da ni kuma bai bar ni ni kadai ba, domin kullum ina yin abubuwan da suke faranta masa rai.”
30Sa'adda Yesu ya ke fadin wadannan abubuwa, dayawa suka bada gaskiya gare shi.
31Yesu ya gayawa wadancan Yahudawa da suka bada gaskiya gare shi, “Idan kun tsaya a cikin magana ta ku almajiraina ne na gaskiya,
32Kuma za ku san gaskiya, gaskiya kuwa zata 'yantar da ku.”
33Suka amsa masa, “Mu zuriyar Ibrahim ne kuma bamu taba yin bauta wurin kowa ba, yaya za ka ce, 'Za a 'yantar da ku'?”
34Yesu ya ce masu, “Hakika, hakika, ina ce maku, dukan wanda ya ke aika zunubi bawan zunubi ne.
35Bawa kuwa, ba ya zama a gida dindindin, da yana zama dindindin.
36Saboda haka, idan Dan ya 'yantar da ku zaku zama 'yantattu sosai.
37Na san ku zuriyar Ibrahim ne, kuna so ku kashe ni saboda kalma ta bata da wurin zama a cikin ku.

Read Yahaya 8Yahaya 8
Compare Yahaya 8:22-37Yahaya 8:22-37