Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Yahaya - Yahaya 8

Yahaya 8:17-28

Help us?
Click on verse(s) to share them!
17I, a cikin dokarku an rubuta cewa shaidar mutum biyu gaskiya ce.
18Ni ne ni ke shaidar kaina, kuma Uba wanda ya aiko ni ya na shaida ta.
19Su ka ce da shi, “Ina ubanka?” Yesu ya amsa ma su ya ce, “baku san ni ba balle Ubana, in da kun san ni da kun san Uba na kuma.”
20Ya fadi wadannan kalmomi a kusa da wurin ajiya sa'adda ya ke koyarwa a cikin haikali, kuma ba wanda ya kama shi saboda sa'arsa bata yi ba tukuna.
21Ya kara cewa da su, “Zan tafi, za ku neme ni ba za ku same ni ba, za ku mutu cikin zunubinku. Inda ni ke tafiya, ba za ku iya zuwa ba”.
22Yahudawa su ka ce, “Zai kashe kansa ne, da ya ce inda ni ke tafiya ba za ku iya zuwa ba?”
23Yesu ya ce masu ku daga kasa kuke, Ni kuwa daga bisa ni ke. Ku na wannan duniya ne, Ni kuwa ba na wannan duniya ba ne.
24Shiyasa na ce maku za ku mutu cikin zunubanku. In ba kun bada gaskiya NI NE ba, za ku mutu cikin zunubanku.
25Sai kuma suka ce da shi, “Wanene kai?” Yesu ya ce masu, “Abin da na gaya maku tun daga farko.
26Ina da a bubuwa da yawa da zan gaya maku, in kuma hukunta ku a kai. Duk da haka, wanda ya aiko ni, mai gaskiya ne, abubuwan da naji daga wurin sa, wadannan abubuwan su ni ke gaya wa duniya.”
27Ba su gane ba yana yi masu magana a kan Uban.
28Yesu ya ce, “Sa'adda kuka tada Dan Mutum sama sa'annan za ku gane NI NE, kuma ban yi komi domin kaina ba. Kamar yadda Uba ya koya mani, haka nike fadin wadannan abubuwa.

Read Yahaya 8Yahaya 8
Compare Yahaya 8:17-28Yahaya 8:17-28