Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Yahaya - Yahaya 8

Yahaya 8:14-23

Help us?
Click on verse(s) to share them!
14Yesu ya amsa ya ce masu, “Ko ma na bada shaida a kai na, shaidata gaskiya ce, na san daga inda na fito da inda zan tafi, amma ku baku san daga inda na fito ba, baku kuma san inda zan tafi ba.
15Kuna shari'a ta son kai, ni ko ban yi wa kowa shari'a ba.
16Ko ma da na yi shari'a, shari'ata gaskiya ce domin ba ni kadai ba ne, amma ina tare da Uba wanda ya aiko ni.
17I, a cikin dokarku an rubuta cewa shaidar mutum biyu gaskiya ce.
18Ni ne ni ke shaidar kaina, kuma Uba wanda ya aiko ni ya na shaida ta.
19Su ka ce da shi, “Ina ubanka?” Yesu ya amsa ma su ya ce, “baku san ni ba balle Ubana, in da kun san ni da kun san Uba na kuma.”
20Ya fadi wadannan kalmomi a kusa da wurin ajiya sa'adda ya ke koyarwa a cikin haikali, kuma ba wanda ya kama shi saboda sa'arsa bata yi ba tukuna.
21Ya kara cewa da su, “Zan tafi, za ku neme ni ba za ku same ni ba, za ku mutu cikin zunubinku. Inda ni ke tafiya, ba za ku iya zuwa ba”.
22Yahudawa su ka ce, “Zai kashe kansa ne, da ya ce inda ni ke tafiya ba za ku iya zuwa ba?”
23Yesu ya ce masu ku daga kasa kuke, Ni kuwa daga bisa ni ke. Ku na wannan duniya ne, Ni kuwa ba na wannan duniya ba ne.

Read Yahaya 8Yahaya 8
Compare Yahaya 8:14-23Yahaya 8:14-23