Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Yahaya - Yahaya 8

Yahaya 8:1-41

Help us?
Click on verse(s) to share them!
1Yesu ya je Dutsen Zaitun.
2Da sassafe ya dawo Haikali, dukan mutane kuma suka zo wurin sa; yazauna koya masu.
3Sai marubuta da Farisawa suka kawo mace wadda aka kama ta tana zina. Su ka sa ta a tsakiya.
4Sai su ka ce da shi, “Malam, wannan mace an kama ta tana cikin yin zina.
5A cikin shari'a, Musa ya bamu umurni mu jejjefe irin wandannan mutume, kai me ka ce game da ita?”
6Sun fadi haka ne domin su gwada shi su sami abinda za su zarge shi da shi, amma Yesu ya sunkuya yayi rubutu da yatsansa a kasa.
7Sa'adda suka cigaba da tambayar sa, ya mike tsaye yace masu, “shi wanda ba shi da zunubi a cikin ku, ya fara jifar ta da dutse.”
8Ya sake sunkuyawa, ya yi rubutu da yatsansa a kasa.
9Da suka ji haka, sai suka fita dai-dai da dai-dai, kama daga babbansu. A karshe dai aka bar Yesu shi kadai, tare da matar wadda ta ke a tsakiyar su.
10Yesu ya tashi tsaye ya ce da ita, “mace, ina masu zargin ki? Ba wanda ya kashe ki?
11Ta ce, “Ba kowa, Ubangiji” Yesu ya ce, “Ni ma ban kashe ki ba. Ki yi tafiyar ki, daga yanzu kada ki kara yin zunubi.”
12Yesu ya kara yin magana da mutanen cewa, “Ni ne hasken duniya, shi wanda ya biyo ni, ba zai yi tafiya cikin duhu ba, amma za ya sami hasken rai.
13Farisawa suka ce masa, “Kana bada shaida a kan ka, shaidarka ba gaskiya ba ce.”
14Yesu ya amsa ya ce masu, “Ko ma na bada shaida a kai na, shaidata gaskiya ce, na san daga inda na fito da inda zan tafi, amma ku baku san daga inda na fito ba, baku kuma san inda zan tafi ba.
15Kuna shari'a ta son kai, ni ko ban yi wa kowa shari'a ba.
16Ko ma da na yi shari'a, shari'ata gaskiya ce domin ba ni kadai ba ne, amma ina tare da Uba wanda ya aiko ni.
17I, a cikin dokarku an rubuta cewa shaidar mutum biyu gaskiya ce.
18Ni ne ni ke shaidar kaina, kuma Uba wanda ya aiko ni ya na shaida ta.
19Su ka ce da shi, “Ina ubanka?” Yesu ya amsa ma su ya ce, “baku san ni ba balle Ubana, in da kun san ni da kun san Uba na kuma.”
20Ya fadi wadannan kalmomi a kusa da wurin ajiya sa'adda ya ke koyarwa a cikin haikali, kuma ba wanda ya kama shi saboda sa'arsa bata yi ba tukuna.
21Ya kara cewa da su, “Zan tafi, za ku neme ni ba za ku same ni ba, za ku mutu cikin zunubinku. Inda ni ke tafiya, ba za ku iya zuwa ba”.
22Yahudawa su ka ce, “Zai kashe kansa ne, da ya ce inda ni ke tafiya ba za ku iya zuwa ba?”
23Yesu ya ce masu ku daga kasa kuke, Ni kuwa daga bisa ni ke. Ku na wannan duniya ne, Ni kuwa ba na wannan duniya ba ne.
24Shiyasa na ce maku za ku mutu cikin zunubanku. In ba kun bada gaskiya NI NE ba, za ku mutu cikin zunubanku.
25Sai kuma suka ce da shi, “Wanene kai?” Yesu ya ce masu, “Abin da na gaya maku tun daga farko.
26Ina da a bubuwa da yawa da zan gaya maku, in kuma hukunta ku a kai. Duk da haka, wanda ya aiko ni, mai gaskiya ne, abubuwan da naji daga wurin sa, wadannan abubuwan su ni ke gaya wa duniya.”
27Ba su gane ba yana yi masu magana a kan Uban.
28Yesu ya ce, “Sa'adda kuka tada Dan Mutum sama sa'annan za ku gane NI NE, kuma ban yi komi domin kaina ba. Kamar yadda Uba ya koya mani, haka nike fadin wadannan abubuwa.
29Shi wanda ya aiko ni, yana tare da ni kuma bai bar ni ni kadai ba, domin kullum ina yin abubuwan da suke faranta masa rai.”
30Sa'adda Yesu ya ke fadin wadannan abubuwa, dayawa suka bada gaskiya gare shi.
31Yesu ya gayawa wadancan Yahudawa da suka bada gaskiya gare shi, “Idan kun tsaya a cikin magana ta ku almajiraina ne na gaskiya,
32Kuma za ku san gaskiya, gaskiya kuwa zata 'yantar da ku.”
33Suka amsa masa, “Mu zuriyar Ibrahim ne kuma bamu taba yin bauta wurin kowa ba, yaya za ka ce, 'Za a 'yantar da ku'?”
34Yesu ya ce masu, “Hakika, hakika, ina ce maku, dukan wanda ya ke aika zunubi bawan zunubi ne.
35Bawa kuwa, ba ya zama a gida dindindin, da yana zama dindindin.
36Saboda haka, idan Dan ya 'yantar da ku zaku zama 'yantattu sosai.
37Na san ku zuriyar Ibrahim ne, kuna so ku kashe ni saboda kalma ta bata da wurin zama a cikin ku.
38Na fadi abubuwan da na gani a wurin Ubana, ku kuma kuna yin abubuwan da kuka ji daga wurin ubanku.”
39Suka amsa suka ce masa, “Ibrahim ne ubanmu” Yesu ya ce masu, “Da ku 'yayan Ibrahim ne da kun yi ayukan da Ibrahim ya yi.
40Amma, yanzu kuna so ku kashe ni, mutumin da ya gaya maku gaskiyar da ya ji daga wurin Allah. Ibrahim bai yi haka ba.
41Kuna yin ayyukan ubanku. Suka ce masa, “mu ba a haife mu cikin fasikanci ba, muna da Uba daya: Allah.”

Read Yahaya 8Yahaya 8
Compare Yahaya 8:1-41Yahaya 8:1-41