Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Yahaya - Yahaya 7

Yahaya 7:36-52

Help us?
Click on verse(s) to share them!
36Wace kalma ya ke fadi haka, 'za ku neme ni amma ba za ku same ni ba; inda na tafi, ba za ku iya zuwa ba'?”
37To a rana ta karshe, babbar rana ta idin, Yesu ya mike ya yi magana da karfi cewa, “Idan kowa yana jin kishi, ya zo wuri na ya sha.
38Shi wanda ya bada gaskiya gare ni kamar yadda nassi ya fadi, daga cikin sa rafukan ruwa na rai za su bulbulo.”
39Amma ya fadi haka a kan Ruhu, wanda wadanda suka bada gaskiya gare shi za su karba; ba a ba da Ruhun ba tukuna, saboda ba a rigaya an daukaka Yesu ba.
40Wadansu a cikin taron, sa'anda suka ji wadannan kalmomi, suka ce, “Wannan lallai annabi ne.”
41Wadansu suka ce, “Wannan Almasihu ne.” Amma wadansu suka ce, “Almasihu zai fito daga Gallili ne.?
42Ba nassi ya ce Almasihu zai fito daga cikin dangin Dauda daga Baitalami ba, daga kauyen da Dauda ya fito?”
43Sai aka sami rabuwa a cikin taron saboda shi.
44Da wadansun su sun kama shi, amma ba wanda ya sa masa hannu.
45Sa'annan jami'an suka dawo wurin manyan Fristoci da Farisawa, wadanda suka ce,” me yasa ba ku kawo shi ba?”
46Jami'an su ka amsa, “Ba mutumin da ya taba yin magana kamar haka.”
47Farisawa suka amsa masu, “kuma an karkatar da ku?
48Ko wani daga cikin mahukunta ya bada gaskiya gare shi, ko kuwa daga cikin Farisawa?
49Amma wannan taro da basu san shari'a ba, la'anannu ne.”
50Nikodimus ya ce masu, (shi wanda ya zo wurin Yesu da, daya daga cikin Farisawa),
51“Ko shari'armu bata hana hukunta mutum ba, sai ta ji daga gare shi ta kuma san abin da ya aikata ba?”
52Suka amsa masa suka ce, “kai ma daga Galili ka fito? Ka yi bincike ka gani ba annanbin da zai fito daga Galili.”

Read Yahaya 7Yahaya 7
Compare Yahaya 7:36-52Yahaya 7:36-52