Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Yahaya - Yahaya 7

Yahaya 7:2-25

Help us?
Click on verse(s) to share them!
2To Idin Bukkoki na Yahudawa ya kusa.
3Sai 'yan'uwansa suka ce da shi, “ka tashi ka tafi Yahudiya, domin almajiranka su ga ayyukan da kake yi su ma.
4Ba wanda ya ke yin wani abu a boye idan dai yana so kowa da kowa ya san shi. Da yake ka na yin wadannan abubuwa sai ka nuna kan ka a fili ga duniya.
5Domin ko 'yan'uwansa ma basu bada gaskiya gare shi ba.
6Yesu ya ce dasu, “lokaci na bai yi ba tukuna, amma ku koyaushe lokacin ku ne.
7Duniya baza ta iya kin ku ba, amma ta ki ni saboda ina fadin cewa ayyukanta ba su da kyau.
8Ku ku je wurin idin, ni ba zan je wurin idin ba domin lokacina bai yi ba tukuna.
9Bayan da ya gaya masu wadannan abubuwa, ya tsaya a cikin Gallili.
10Amma bayan da 'yan'uwansa su ka tafi wurin idin shi ma ya tafi, amma a asirce ba a fili ba.
11Saboda Yahudawa suna neman sa a wurin idin, su na cewa “Ina yake?”
12Akwai maganganu dayawa a kansa cikin taron. Wadansu suna cewa, “shi mutumin kirki ne.” Wadansu kuma suna cewa, “A'a yana karkatar da hankalin jama'a.”
13Amma duk da haka ba wanda ya yi magana a fili a kansa saboda suna jin tsoron Yahudawa.
14Sa'anda aka kai rabin idin, sai Yesu ya shiga cikin haikali ya fara koyarwa.
15Yahudawa suna mamaki suna cewa, “Yaya aka yi wannan mutum ya sami ilimi dayawa haka? Shi kuwa bai je makaranta ba.”
16Yesu ya ba su amsa ya ce, “Koyarwata ba tawa ba ce, amma ta wanda ya aiko ni ce.”
17Idan wani yana so ya yi nufinsa, za ya gane koyarwannan ko daga wurin Allah ta zo, ko ko tawa ce ta kaina.
18Ko wanene yake maganar kansa, yana neman darajar kansa kenan, amma ko wanene ya nemi darajar wanda ya aiko ni, wannan mutum mai gaskiya ne, babu rashin adalci a cikin sa.
19Ba Musa ya baku dokoki ba? Amma duk da haka ba mai aikata dokokin. Me yasa ku ke so ku kashe ni?
20Taron suka ba shi amsa, “Ka na da aljani. Wanene yake so ya kashe ka?”
21Yesu ya amsa ya ce masu, “Nayi aiki daya, dukan ku kuna mamaki da shi.
22Musa ya baku kaciya, {ba kuwa daga Musa take ba, amma daga kakannin kakanni ta ke}, kuma a ranar Asabar kukan yi wa mutum kaciya.
23Idan mutum ya karbi kaciya ranar Asabar, domin kada a karya dokar Musa, don me kuka ji haushi na saboda na mai da mutum lafiyayye sarai ranar Asabar?
24Kada ku yi shari'a ta ganin ido, amma ku yi shari'a mai adalci.”
25Wadansun su daga Urushalima suka ce, “wannan ba shine wannan da suke nema su kashe ba?”

Read Yahaya 7Yahaya 7
Compare Yahaya 7:2-25Yahaya 7:2-25