Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Yahaya - Yahaya 7

Yahaya 7:14-52

Help us?
Click on verse(s) to share them!
14Sa'anda aka kai rabin idin, sai Yesu ya shiga cikin haikali ya fara koyarwa.
15Yahudawa suna mamaki suna cewa, “Yaya aka yi wannan mutum ya sami ilimi dayawa haka? Shi kuwa bai je makaranta ba.”
16Yesu ya ba su amsa ya ce, “Koyarwata ba tawa ba ce, amma ta wanda ya aiko ni ce.”
17Idan wani yana so ya yi nufinsa, za ya gane koyarwannan ko daga wurin Allah ta zo, ko ko tawa ce ta kaina.
18Ko wanene yake maganar kansa, yana neman darajar kansa kenan, amma ko wanene ya nemi darajar wanda ya aiko ni, wannan mutum mai gaskiya ne, babu rashin adalci a cikin sa.
19Ba Musa ya baku dokoki ba? Amma duk da haka ba mai aikata dokokin. Me yasa ku ke so ku kashe ni?
20Taron suka ba shi amsa, “Ka na da aljani. Wanene yake so ya kashe ka?”
21Yesu ya amsa ya ce masu, “Nayi aiki daya, dukan ku kuna mamaki da shi.
22Musa ya baku kaciya, {ba kuwa daga Musa take ba, amma daga kakannin kakanni ta ke}, kuma a ranar Asabar kukan yi wa mutum kaciya.
23Idan mutum ya karbi kaciya ranar Asabar, domin kada a karya dokar Musa, don me kuka ji haushi na saboda na mai da mutum lafiyayye sarai ranar Asabar?
24Kada ku yi shari'a ta ganin ido, amma ku yi shari'a mai adalci.”
25Wadansun su daga Urushalima suka ce, “wannan ba shine wannan da suke nema su kashe ba?”
26Kuma duba, yana magana a fili, sannan ba wanda ya ce da shi komai. Ba zai yiwu ba mahukunta su sani cewa wannan Kristi ne, ko ba haka ba?
27da haka, mun san inda wannan mutum ya fito. Amma sa'anda Kristi za ya zo, ba wanda zai san inda ya fito.”
28Yesu yayi magana da karfi a haikali, yana koyarwa ya na cewa, “Kun san ni kuma kun san inda na fito. Ban zo domin kaina ba, amma wanda ya aiko ni mai gaskiya ne, ku kuwa baku san shi ba.
29Ni na san shi domin daga wurinsa na fito, kuma shine ya aiko ni.”
30Suna kokari su kama shi, amma ba wanda ya iya sa masa hannu domin sa'arsa ba ta yi ba tukuna.
31Duk da haka wadansu dayawa a cikin taron suka bada gaskiya gare shi suka ce, “Sa'anda Kristi ya zo, zai yi alamu fiye da wadanda wannan mutum ya yi?”
32Farisawa suka ji tattarmukan suna yin rada a kan wadannan abubuwa game da Yesu, Sai manyan malamai da Farisawa su ka aika jami'ai su kama shi.
33Sa'annan Yesu yace ma su,” jimawa kadan ina tare ku, sa'annan in tafi wurin wanda ya aiko ni.
34Za ku neme ni ba za ku same ni ba; inda na tafi, ba za ku iya zuwa ba.”
35Yahudawa fa su ka cewa junan su, “Ina wannan mutum zai je inda ba za mu iya samun sa ba? Ko za ya tafi wurin Helinawa na warwatsuwa ya koyawa Helinawa?
36Wace kalma ya ke fadi haka, 'za ku neme ni amma ba za ku same ni ba; inda na tafi, ba za ku iya zuwa ba'?”
37To a rana ta karshe, babbar rana ta idin, Yesu ya mike ya yi magana da karfi cewa, “Idan kowa yana jin kishi, ya zo wuri na ya sha.
38Shi wanda ya bada gaskiya gare ni kamar yadda nassi ya fadi, daga cikin sa rafukan ruwa na rai za su bulbulo.”
39Amma ya fadi haka a kan Ruhu, wanda wadanda suka bada gaskiya gare shi za su karba; ba a ba da Ruhun ba tukuna, saboda ba a rigaya an daukaka Yesu ba.
40Wadansu a cikin taron, sa'anda suka ji wadannan kalmomi, suka ce, “Wannan lallai annabi ne.”
41Wadansu suka ce, “Wannan Almasihu ne.” Amma wadansu suka ce, “Almasihu zai fito daga Gallili ne.?
42Ba nassi ya ce Almasihu zai fito daga cikin dangin Dauda daga Baitalami ba, daga kauyen da Dauda ya fito?”
43Sai aka sami rabuwa a cikin taron saboda shi.
44Da wadansun su sun kama shi, amma ba wanda ya sa masa hannu.
45Sa'annan jami'an suka dawo wurin manyan Fristoci da Farisawa, wadanda suka ce,” me yasa ba ku kawo shi ba?”
46Jami'an su ka amsa, “Ba mutumin da ya taba yin magana kamar haka.”
47Farisawa suka amsa masu, “kuma an karkatar da ku?
48Ko wani daga cikin mahukunta ya bada gaskiya gare shi, ko kuwa daga cikin Farisawa?
49Amma wannan taro da basu san shari'a ba, la'anannu ne.”
50Nikodimus ya ce masu, (shi wanda ya zo wurin Yesu da, daya daga cikin Farisawa),
51“Ko shari'armu bata hana hukunta mutum ba, sai ta ji daga gare shi ta kuma san abin da ya aikata ba?”
52Suka amsa masa suka ce, “kai ma daga Galili ka fito? Ka yi bincike ka gani ba annanbin da zai fito daga Galili.”

Read Yahaya 7Yahaya 7
Compare Yahaya 7:14-52Yahaya 7:14-52