Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Yahaya - Yahaya 6

Yahaya 6:47-65

Help us?
Click on verse(s) to share them!
47Hakika, hakika, wanda ya bada gaskiya, yana da rai Madawwami.
48Ni ne Gurasa ta rai.
49Ubanninku sun ci manna cikin jeji, suka kuma mutu.
50Ga gurasa da ta sauko daga sama, domin mutum ya ci daga cikinta ba kuwa zai mutu ba.
51Ni ne gurasa mai rai da ya sauko daga sama. Duk wanda ya ci daga gurasar, zai rayu har abada. Wannan gurasar da zan bayar jiki na ne don ceton duniya.”
52Sai Yahudawa suka fusata a tsakanin junansu suka kuma fara gardama, cewa, “Yaya mutumin nan zai iya bamu naman jikinsa mu ci?
53Sai Yesu ya ce masu, “hakika, hakika, in ba ku ci naman jikin Dan mutum ba, ba ku kuma sha jininsa ba, ba za ku sami rai a cikin ku ba.
54Dukan wanda ya ci nama na ya kuma sha jinina yana da rai Madawwami, ni kuwa zan tashe shi a ranar karshe.
55Domin namana abinci ne na gaske, jinina kuma abin sha ne na gaskiya.
56Duk wanda ya ci namana, ya kuma sha jinina yana zamne a ciki na, ni kuma a cikinsa.
57Kamar yadda rayayyen Uba ya aiko ni, nake kuma rayuwa saboda Uban, haka ma wanda ya ci namana, zai rayu sabo da ni.
58Wannan itace gurasar da ta sauko daga sama, ba irin wadda Ubanninku suka ci suka mutu ba. Dukan wanda ya ci gurasar zai rayu har abada.”
59Yesu ya fadi wadan nan abubuwa a cikin majami'a sa'ad da yake koyarwa a Kafarnahum.
60Da jin haka, da yawa daga cikin almajiransa suka ce, “Wannan Magana yana da karfi, wa zai iya jinta?”
61Yesu, kuwa da yake ya sani a ransa da cewa almajiransa suna gunagunin wannan, sai ya ce masu, “Wannan ya zamar maku laifi?
62Yaya Ke nan in kun ga Dan Mutum yana hawa inda yake a da?
63Ruhu shine mai bayar da rai; Jiki ba ya amfana komai. Kalmomin da na fada maku ruhu ne, da kuma rai.
64Amma fa akwai wadansun ku da ba su ba da gaskiya ba. Domin tun farko Yesu ya san wadanda ba su ba da gaskiya ba, da kuma wanda zai bashe shi.
65Ya fada cewa, “shiyasa na gaya maku, ba mai iya zuwa wurina, sai ta wurin Uban.”

Read Yahaya 6Yahaya 6
Compare Yahaya 6:47-65Yahaya 6:47-65