Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Yahaya - Yahaya 6

Yahaya 6:4-18

Help us?
Click on verse(s) to share them!
4(Kuma da idin Ketarewa, wato idin Yahudawa, ya kusato.)
5Da Yesu ya daga kai sai ya ga babban taro yana zuwa wurinsa, sai ya ce ma Filibus, “Ina za mu sayi gurasar da Mutanen nan za su ci?”
6(Ya fadi haka ne domin ya gwada shi, saboda shi kansa ya san abin da zai yi.)
7Filibus ya amsa masa, “gurasar dinari biyu ma ba zata ishi kowannensu ya samu ko kadan ba.”
8Daya daga cikin almajiransa, wato Andarawus, dan'uwan Siman Bitrus, ya ce masa,
9“Ga wani dan yaro nan da dunkule biyar na sha'ir, da kifi biyu. Amma menene wadannan za su yi wa mutane masu yawa?”
10Yesu ya ce, “ku sa mutane su zauna.” (wurin kuwa akwai ciyawa.) Sai mazajen suka zauna, sun kai wajen dubu biyar.
11Sai Yesu ya dauki gurasar, bayan da ya yi godiya, sai ya rarraba wa wadanda suke zaune. Haka kuma ya rarraba kifin gwargwadon abin da zai ishe su.
12Da Mutanen suka ci suka kuma koshi, sai ya ce wa almajiransa, ku tattara gutsattsarin da suka rage, kada ya zama asara.”
13Sai suka cika kwanduna goma sha biyu da gutsattsarin gurasar nan biyar da ya rage bayan da kowa ya ci.
14Da jama'a suka ga alamar da ya yi, sai suka ce, “Hakika wannan shi ne annabin nan mai zuwa cikin duniya.
15“Da Yesu ya gane suna shirin zuwa su dauke shi da karfi da yaji su nada shi sarki, sai ya sake komawa kan dutsen da kansa.
16Da yamma ta yi, sai almajiransa suka gangara teku.
17Suka shiga cikin jirgi, suka haye teku zuwa kafarnahum. (A lokacin duhu ya yi, Yesu kuwa bai riga ya iso wurinsu ba tukuna.)
18Iska mai karfin gaske tana kadawa, kuma tekun yana hargowa.

Read Yahaya 6Yahaya 6
Compare Yahaya 6:4-18Yahaya 6:4-18