Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Yahaya - Yahaya 6

Yahaya 6:30-57

Help us?
Click on verse(s) to share them!
30Sai suka ce masa, “To wace alama za ka yi, don mu gani mu gaskata ka?
31Me za ka yi? Kakanninmu sun ci manna a jeji, kamar yadda aka rubuta, “Ya ba su gurasa daga sama su ci.”
32Sa'an nan Yesu ya ce masu, “hakika, hakika, ina gaya maku ba Musa ne ya ba ku gurasa nan daga sama ba, amma Ubana ne ya baku gurasa ta gaskiya daga sama.
33Gurasar Allah itace mai saukowa daga sama mai kuma bada rai ga duniya,”
34Sai suka ce masa, “Mallam, ka rika ba mu irin wannan gurasa kodayaushe.”
35Yesu ya ce masu, “Ni ne gurasa mai ba da rai. Wanda ya zo wurina ba zai ji yunwa ba, wanda kuma ya gaskanta da ni ba zai kara jin kishi ba.
36Amma na gaya maku cewa, hakika kun gan ni, duk da haka ba ku ba da gaskiya ba.
37Duk wanda Uba ya bani zai zo gare ni, wanda kuwa ya zo gare ni ba zan kore shi ba ko kadan.
38Gama na sauko daga sama, ba domin in bi nufin kaina ba, sai dai nufin wanda ya aiko ni.
39Wannan shi ne nufin wanda ya aiko ni, kada in rasa ko daya daga cikin wadannan da ya bani, sai dai in tashe su a ranar karshe.
40Gama wannan shi ne nufin Ubana, duk wanda yake ganin Dan ya kuma gaskata da shi zai sami rai madawwami, ni kuma zan tashe shi a ranar karshe.
41Sai Yahudawa suka yi gunaguni akansa, domin ya ce, “Nine Gurasar da ta sauko daga sama.”
42Suka ce, “Ba wannan ne Yesu Dan Yusufu, wanda Ubansa da Uwarsa mun san su ba? Ta yaya yanzu zai ce, 'Na ya sauko daga sama'?
43Yesu ya amsa, ya ce masu, “Kada ku yi gunaguni a junanku.
44Ba mai iya zuwa wurina sai dai in Uba wanda ya aiko ni ya jawo shi, ni kuwa zan tashe shi a rana ta karshe.
45A rubuce yake cikin litattafan anabawa cewa, 'Dukkansu Allah zai koya masu'. Duk wanda ya ji ya kuma koya daga wurin Uba, ya kan zo gare ni.
46Ba cewa wani ya taba ganin Uban ba, sai shi wanda yake daga wurin Allah - shine ya ga Uban.
47Hakika, hakika, wanda ya bada gaskiya, yana da rai Madawwami.
48Ni ne Gurasa ta rai.
49Ubanninku sun ci manna cikin jeji, suka kuma mutu.
50Ga gurasa da ta sauko daga sama, domin mutum ya ci daga cikinta ba kuwa zai mutu ba.
51Ni ne gurasa mai rai da ya sauko daga sama. Duk wanda ya ci daga gurasar, zai rayu har abada. Wannan gurasar da zan bayar jiki na ne don ceton duniya.”
52Sai Yahudawa suka fusata a tsakanin junansu suka kuma fara gardama, cewa, “Yaya mutumin nan zai iya bamu naman jikinsa mu ci?
53Sai Yesu ya ce masu, “hakika, hakika, in ba ku ci naman jikin Dan mutum ba, ba ku kuma sha jininsa ba, ba za ku sami rai a cikin ku ba.
54Dukan wanda ya ci nama na ya kuma sha jinina yana da rai Madawwami, ni kuwa zan tashe shi a ranar karshe.
55Domin namana abinci ne na gaske, jinina kuma abin sha ne na gaskiya.
56Duk wanda ya ci namana, ya kuma sha jinina yana zamne a ciki na, ni kuma a cikinsa.
57Kamar yadda rayayyen Uba ya aiko ni, nake kuma rayuwa saboda Uban, haka ma wanda ya ci namana, zai rayu sabo da ni.

Read Yahaya 6Yahaya 6
Compare Yahaya 6:30-57Yahaya 6:30-57