Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Yahaya - Yahaya 6

Yahaya 6:21-35

Help us?
Click on verse(s) to share them!
21Sa'an nan suka yarda suka karbe shi a cikin jirgin, kuma nan da nan jirgin ya kai gacci.
22Kashe gari, sauran taron da suke tsaye a dayan hayin tekun suka ga cewa babu wani jirgi a wajen sai dayan, Yesu kuma bai shiga ciki da almajiransa ba, amma almajiransa suka tafi su kadai.
23Sai dai, akwai wadansu jirage da suka zo daga Tibariya kusa da wurin da taron suka ci gurasa bayan da Ubangiji ya yi godiya.
24Sa'anda taron suka gane cewa Yesu da almajiransa ba su wurin, su da kansu su ka shiga cikin jiragen suka tafi Kafarnahum neman Yesu.
25Da suka same shi a hayin tekun, suka ce masa, “Mallam, yaushe ka zo nan?”
26Yesu ya amsa masu, da cewa, “hakika, kuna nema na ne, ba don kun ga alamu ba, amma domin kun ci gurasar nan kun koshi.
27Ku daina yin wahala a kan neman abinci mai lalacewa, sai dai a kan abinci mai dawwama wanda zai kaiku ga rai madawwami wanda Dan Mutum zai ba ku, domin Ubangiji Allah ya sa hatiminsa a kansa.”
28Sai suka ce Masa, “Me za mu yi, domin mu aikata ayyukan Allah?
29Yesu ya amsa, “Wannan shi ne aikin Allah: wato ku gaskata da wanda ya aiko.”
30Sai suka ce masa, “To wace alama za ka yi, don mu gani mu gaskata ka?
31Me za ka yi? Kakanninmu sun ci manna a jeji, kamar yadda aka rubuta, “Ya ba su gurasa daga sama su ci.”
32Sa'an nan Yesu ya ce masu, “hakika, hakika, ina gaya maku ba Musa ne ya ba ku gurasa nan daga sama ba, amma Ubana ne ya baku gurasa ta gaskiya daga sama.
33Gurasar Allah itace mai saukowa daga sama mai kuma bada rai ga duniya,”
34Sai suka ce masa, “Mallam, ka rika ba mu irin wannan gurasa kodayaushe.”
35Yesu ya ce masu, “Ni ne gurasa mai ba da rai. Wanda ya zo wurina ba zai ji yunwa ba, wanda kuma ya gaskanta da ni ba zai kara jin kishi ba.

Read Yahaya 6Yahaya 6
Compare Yahaya 6:21-35Yahaya 6:21-35