Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Yahaya - Yahaya 5

Yahaya 5:22-37

Help us?
Click on verse(s) to share them!
22Gama Uban ba ya hukunta kowa, sai dai ya damka dukan hukunci ga Dan,
23domin kowa ya girmama Dan, kamar yadda suke girmama Uban. Shi wanda ba ya girmama Dan, ba ya girmama Uban da ya aiko shi.
24Hakika, hakika, duk mai jin Maganata, yana kuma gaskata wanda ya aiko ni, yana da rai madawwami ba kuma za a kashe shi ba, domin ya ratse daga mutuwa zuwa rai.
25Hakika hakika, ina gaya maku, lokaci na zuwa, har ma ya yi da matattatu za su ji muryar Dan Allah, wadanda suka ji kuwa za su rayu.
26Kammar yada Uba ya ke da rai a cikinsa, haka ya ba Dan don ya zama da rai cikin kansa.
27Uban ya kuma ba Dan ikon zartar da hukunci, saboda shi ne Dan Mutum.
28Kada ku yi mamakin wannan, domin lokaci na zuwa da duk wadanda suke kaburbura za su ji muryarsa,
29su kuma fito: wadanda suka aikata nagarta zawa tashi na rai, wadanda suka aikata mugunta kuwa zuwa tashi na hukunci.
30Ba na iya yin kome ni da kai na. Yadda na ke ji, haka nake yin hukunci, Hukunci na kuwa na adalci ne, domin ba nufin kaina nake bi ba, sai dai nufin wanda ya aiko ni.
31Idan zan yi shaida game da kaina, shaidata baza ta zama gaskiya ba.
32Akwai wani wanda ya ke bada shaida game da ni, na kuwa sani shaidar da yake bayarwa game da ni gaskiya ce.
33Kun aika zuwa wurin Yahaya, shi kuma ya yi shaidar gaskiya.
34Duk da haka shaidar da na karba bata mutum bace. Na fadi wadanan abubuwa domin ku sami ceto.
35Yahaya fitila ne mai ci, mai haske ne kuma, kun yarda ku yi farinciki da haskensa dan lokaci kadan.
36Amma shaidar da ni ke da ita ta fi ta Yahaya karfi. Domin ayyukan da Uba ya bani ni in yi, wato ainihin ayyukan da nake yi, su ne suke shaida ta cewa, Uba ne ya aiko ni.
37Uba wanda ya aiko ni, shi da kansa ya shaide ni. Ba ku taba jin muryar sa ba, ko ganin kamanninsa.

Read Yahaya 5Yahaya 5
Compare Yahaya 5:22-37Yahaya 5:22-37