Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Yahaya - Yahaya 5

Yahaya 5:2-25

Help us?
Click on verse(s) to share them!
2To a cikin Urashilima kusa da kofar tumaki akwai tabki, wanda ake kira Baitasda da harshen Ibraniyanci, yana da shirayi biyar.
3Taron mutane dayawa masu ciwo da, makafi da guragu da shanyayyu suna kwance a wurin suna jira a dama ruwan.
4Gama mala'ikan Ubangiji kan sabko a cikin tabkin ya dama ruwan, wanda ya fara taba ruwan sai ya warke komai cutar da yake da ita.
5Akwai wani mutum a bakin tabki yana kwance yana da rashin lafiya har shekara talatin da takwas.
6Da Yesu ya gan shi yana kwance a wurin sai ya gane ya dade a wurin, sai ya ce masa, “Ko kana so ka warke?”
7Sai mai rashin lafiyar ya amsa ya ce, “Malam, bani da kowa da zai sa ni a cikin tabkin idan ruwan ya motsa. Yayinda na ke kokari sai wani ya riga ni.”
8Yesu ya ce masa,” Ka tashi ka dauki shimfidarka ka tafi.”
9Nan dan nan Mutumin ya warke, ya dauki shimfidarsa ya tafi. Ranar kuwa Asabar ce.
10Sai Yahudawa suka ce da wanda aka warkar din, “Ai, Asabar ce, bai kuwa halatta ka dauki shimfidarka ba.”
11Sai ya amsa ya ce, “Ai wanda ya warkar da ni, shine ya ce mani 'Dauki shimfidarka, ka tafi.”
12Suka tambaye shi, “wane mutum ne ya ce maka, 'Dauki shimfidar ka yi tafiya'?”
13Sai dai, shi wanda aka warka din, ba san ko wanene ya warkar da shi ba, domin Yesu ya riga ya tafi aboye, saboda akwai taro a wurin.
14Bayan haka, Yesu ya same shi a Haikalin, ya ce masa, “ka ga fa, ka warke. To, kada ka kara yin zunubi don kada wani abu da ya fi wannan muni ya same ka.”
15Sai mutumin ya tafi ya gaya wa Yahuduwa cewa Yesu ne ya warkar da shi.
16To saboda haka Yahudawa suka fara tsanantawa Yesu, don ya yi wadannan abubuwa ran Asabar.
17Yesu kuwa ya amsa masu ya ce, “Ubana yana aiki har yanzu, ni ma ina aiki.”
18Saboda haka, Yahudawa suka kara nema su kashe shi ba don ya keta Asabar kadai ba, amma kuma domin ya ce Allah Ubansa ne, wato yana maida kansa dai-dai da Allah.
19Yesu ya amsa masu ya ce, hakika hakika, ina gaya maku, Dan ba ya yin kome shi kadai, sai abin da ya ga Uba yana yi.
20Domin Uban na kaunar Dan, yana kuma nuna masa dukan abinda shi da kansa yake yi, kuma zai nuna masa abubuwan da suka fi wadannan, domin ku yi mamaki.
21Gama kamar yadda Uba yakan tada matattu ya kuma basu rai, haka Dan ma yake bada rai ga duk wanda ya nufa.
22Gama Uban ba ya hukunta kowa, sai dai ya damka dukan hukunci ga Dan,
23domin kowa ya girmama Dan, kamar yadda suke girmama Uban. Shi wanda ba ya girmama Dan, ba ya girmama Uban da ya aiko shi.
24Hakika, hakika, duk mai jin Maganata, yana kuma gaskata wanda ya aiko ni, yana da rai madawwami ba kuma za a kashe shi ba, domin ya ratse daga mutuwa zuwa rai.
25Hakika hakika, ina gaya maku, lokaci na zuwa, har ma ya yi da matattatu za su ji muryar Dan Allah, wadanda suka ji kuwa za su rayu.

Read Yahaya 5Yahaya 5
Compare Yahaya 5:2-25Yahaya 5:2-25