Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Yahaya - Yahaya 5

Yahaya 5:12-25

Help us?
Click on verse(s) to share them!
12Suka tambaye shi, “wane mutum ne ya ce maka, 'Dauki shimfidar ka yi tafiya'?”
13Sai dai, shi wanda aka warka din, ba san ko wanene ya warkar da shi ba, domin Yesu ya riga ya tafi aboye, saboda akwai taro a wurin.
14Bayan haka, Yesu ya same shi a Haikalin, ya ce masa, “ka ga fa, ka warke. To, kada ka kara yin zunubi don kada wani abu da ya fi wannan muni ya same ka.”
15Sai mutumin ya tafi ya gaya wa Yahuduwa cewa Yesu ne ya warkar da shi.
16To saboda haka Yahudawa suka fara tsanantawa Yesu, don ya yi wadannan abubuwa ran Asabar.
17Yesu kuwa ya amsa masu ya ce, “Ubana yana aiki har yanzu, ni ma ina aiki.”
18Saboda haka, Yahudawa suka kara nema su kashe shi ba don ya keta Asabar kadai ba, amma kuma domin ya ce Allah Ubansa ne, wato yana maida kansa dai-dai da Allah.
19Yesu ya amsa masu ya ce, hakika hakika, ina gaya maku, Dan ba ya yin kome shi kadai, sai abin da ya ga Uba yana yi.
20Domin Uban na kaunar Dan, yana kuma nuna masa dukan abinda shi da kansa yake yi, kuma zai nuna masa abubuwan da suka fi wadannan, domin ku yi mamaki.
21Gama kamar yadda Uba yakan tada matattu ya kuma basu rai, haka Dan ma yake bada rai ga duk wanda ya nufa.
22Gama Uban ba ya hukunta kowa, sai dai ya damka dukan hukunci ga Dan,
23domin kowa ya girmama Dan, kamar yadda suke girmama Uban. Shi wanda ba ya girmama Dan, ba ya girmama Uban da ya aiko shi.
24Hakika, hakika, duk mai jin Maganata, yana kuma gaskata wanda ya aiko ni, yana da rai madawwami ba kuma za a kashe shi ba, domin ya ratse daga mutuwa zuwa rai.
25Hakika hakika, ina gaya maku, lokaci na zuwa, har ma ya yi da matattatu za su ji muryar Dan Allah, wadanda suka ji kuwa za su rayu.

Read Yahaya 5Yahaya 5
Compare Yahaya 5:12-25Yahaya 5:12-25