Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Yahaya - Yahaya 4

Yahaya 4:4-20

Help us?
Click on verse(s) to share them!
4Amma ya zamar masa dole ya ratsa ta Samariya.
5Ya zo wani birnin Samariya, mai suna Sika, kusa da filin da Yakubu ya ba dansa Yusufu.
6Rijiyar Yakubu na wurin. Da Yesu ya gaji da tafiyarsa sai ya zauna gefen rijiyar. Kusan karfe goma sha biyu na rana ne.
7Wata mace, Ba-Samariya ta zo domin ta dibi ruwa, sai Yesu ya ce mata, “Ba ni ruwa in sha.”
8Gama almajiransa sun tafi cikin gari don sayen abinci.
9Sai ba-Samariyar tace masa, “Yaya kai da kake Bayahude kake tambaya ta ruwan sha, ni da nike 'yar Samariya?” Domin Yahudawa ba su harka da Samariyawa.
10Sai Yesu ya amsa yace mata, “In da kin san kyautar Allah, da shi wanda yake ce da ke, 'Ba ni ruwan sha,' da kin roke shi, sai kuma ya ba ki ruwan rai.”
11Matar tace masa, “Mallam, ga shi ba ka da guga, kuma rijiyar tana da zurfi. Ina za ka samu ruwan rai?
12Ai ba ka fi Ubanmu Yakubu ba, ko ka fi shi, shi wanda ya ba mu rijiyar, shi kansa kuma ya sha daga cikin ta, haka kuma 'ya'yansa da shanunsa?”
13Yesu ya amsa yace mata, “duk wanda ya sha daga wannan ruwan zai sake jin kishi,
14amma duk wanda ya sha daga ruwa da zan ba shi ba zai sake jin kishi ba. Maimakon haka, ruwan da zan bashi zai zama mabulbular ruwa a cikinsa wanda ke bulbula zuwa rai madawwami.”
15Matar tace masa, “Mallam, ka ba ni wannan ruwa yadda ba zan kara jin kishi ba ba kuma sai na zo nan don in dibi ruwa ba.”
16Yesu ya ce mata, “Je, ki kira maigidanki ku zo nan tare.”
17Matar ta amsa tace masa, “Ba ni da miji.” Yesu yace, “Kin fadi daidai da kika ce, 'ba ni da miji,'
18domin kin auri mazaje har biyar, kuma wanda kike da shi yanzu ba mijin ki bane. Abinda kika fada gaskiya ne.”
19Matar tace masa, “Mallam, Na ga kai annabi ne.
20Ubaninmu sun yi sujada a wannan dutse, amma kun ce Urushalima ce wurin da ya kamata mutane su yi sujada.”

Read Yahaya 4Yahaya 4
Compare Yahaya 4:4-20Yahaya 4:4-20