Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Yahaya - Yahaya 4

Yahaya 4:34-52

Help us?
Click on verse(s) to share them!
34Yesu ya ce masu, “Abincina shine in yi nufin wanda ya aiko ni, in kuma cika aikinsa.
35Ba ku kan ce, 'akwai wata hudu tukuna kafin girbi ya zo ba?' Ina gaya maku, daga idanunku ku ga gonakin, sun rigaya sun isa girbi.
36Shi wanda ke girbi yakan karbi sakamako ya kuma tattara amfanin gona zuwa rai na har abada, ta haka shi mai shuka da shi mai girbi za su yi farinciki tare.
37Gama cikin wannan maganar take, 'Wani na shuka, wani kuma na girbi.'
38Na aike ku ku yi girbin abinda ba ku yi aiki a kai ba. Wandansu sun yi aiki, ku kuma kun shiga cikin wahalarsu.
39Yawancin Samariyawan da ke wannan birni suka gaskata da shi sabili da labarin matar data bada shaida, “Ya gaya mani duk abinda na taba yi.”
40To sa'adda Samariyawa suka zo wurinsa, sai suka roke shi ya zauna tare da su, ya kuwa zauna wurin kwana biyu.
41Wasu da dama kuma suka gaskata domin maganarsa.
42Suka cewa matar, “Mun bada gaskiya, ba saboda maganar ki kadai ba, amma mu kanmu munji, yanzu kuma mun sani cewa wannan lallai shine mai ceton duniya.”
43Bayan wadannan kwana biyu, ya bar wurin zuwa Galili.
44Domin Yesu da kansa yace, ba a girmama annabi a kasarsa.
45Da ya zo Galili, Galiliyawan suka marabce shi. Sun ga dukan abubuwan da ya yi a Urushalima wurin idin, domin su ma sun je idin.
46Kuma ya koma Kana ta Galili inda ya mayar da ruwa zuwa ruwan inabi. Akwai wani ma'aikacin fada wanda dansa na rashin lafiya a Kafarnahum.
47Da ya ji cewa Yesu ya bar Yahudiya ya koma Galili, sai ya tafi wurin Yesu ya roke shi ya sauko ya warka da dansa wanda ke bakin mutuwa.
48Yesu yace masa, “Idan ba ku ga alamu da mu'ujizai ba, ba za ku gaskata ba.”
49Ma'aikacin ya ce masa, “Mallam, ka sauko kafin da na ya mutu.”
50Yesu yace masa, “Je ka. Dan ka ya rayu.” Mutumin ya gaskata maganar da Yesu ya gaya masa, Sai yayi tafiyarsa.
51Yayin da yake sauka kasa, bayinsa suka same shi, suna cewa, danka yana raye.
52Sai ya tambaye su sa'ar da ya fara samun sauki. Suka amsa masa, “Jiya a sa'a ta bakwai zazabin ya bar shi.”

Read Yahaya 4Yahaya 4
Compare Yahaya 4:34-52Yahaya 4:34-52