Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Yahaya - Yahaya 4

Yahaya 4:23-36

Help us?
Click on verse(s) to share them!
23Sai dai, sa'a tana zuwa, har ma ta yi, wadda masu sujada na gaskiya za su yi wa Uba sujada a cikin ruhu da gaskiya, domin irin wadannan ne Uban ke nema su zama masu yi masa sujada.
24Allah Ruhu ne, kuma mutanen da ke yi masa sujada, dole su yi sujada cikin ruhu da gaskiya.”
25Matar ta ce masa, “Na san Almasihu na zuwa (wanda ake kira Kristi). Sa'adda ya zo, zai bayyana mana kowane abu.
26Yesu ya ce mata, “Ni ne shi, wanda ke yi maki magana.”
27A daidai wannan lokaci, almajiransa suka dawo. Suna ta mamakin dalilin da yasa yake magana da mace, amma babu wanda yace, “Me kake so?” Ko kuma, “Don me ka ke magana da ita?”
28Sai matar ta bar tulunta, ta koma cikin gari, tace wa mutanen,
29“Ku zo ku ga wani mutum wanda ya gaya mani duk wani abu da na taba yi. Wannan dai ba Almasihun bane, ko kuwa?”
30Suka bar garin suka zo wurinsa.
31A wannan lokacin, almajiransa suna rokansa, cewa, “Mallam, ka ci.”
32Amma ya ce masu, “ina da abinci da ba ku san komai akai ba.”
33Sai almajiran suka ce da junansu, “Babu wanda ya kawo masa wani abu ya ci, ko akwai ne?”
34Yesu ya ce masu, “Abincina shine in yi nufin wanda ya aiko ni, in kuma cika aikinsa.
35Ba ku kan ce, 'akwai wata hudu tukuna kafin girbi ya zo ba?' Ina gaya maku, daga idanunku ku ga gonakin, sun rigaya sun isa girbi.
36Shi wanda ke girbi yakan karbi sakamako ya kuma tattara amfanin gona zuwa rai na har abada, ta haka shi mai shuka da shi mai girbi za su yi farinciki tare.

Read Yahaya 4Yahaya 4
Compare Yahaya 4:23-36Yahaya 4:23-36