Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Yahaya - Yahaya 3

Yahaya 3:3-14

Help us?
Click on verse(s) to share them!
3Yesu ya amsa masa, “Hakika, hakika, idan ba a sake haifuwar mutum ba, ba zai iya ganin mulkin Allah ba.”
4Nikodimu ya ce masa, “Yaya za a sake haifuwar mutum bayan ya tsufa? Ba zai iya sake shiga cikin cikin uwarsa kuma a haife shi ba, zai iya?”
5Yesu ya amsa, “Hakika, hakika, idan ba a haifi mutum da ruwa da kuma Ruhu ba, ba zai iya shiga cikin mulkin Allah ba.
6Abin da aka haifa ta wurin jiki, jiki ne, kuma abin da aka haifa ta wurin Ruhu, Ruhu ne.
7Kada ka yi mamaki don na ce maka, 'dole a maya haifuwar ka.'
8Iska takan hura duk inda ta ga dama. Ka kan ji motsin ta, amma ba ka san inda ta fito ko inda za ta tafi ba. Haka duk wanda aka haifa daga Ruhu.”
9Nikodimu ya amsa yace masa, “Yaya wannan zai yiwu?”
10Yesu ya amsa yace masa, “Kai malami ne a Israila amma ba ka san wadannan al'amura ba?
11Hakika, hakika, ina gaya maka, muna fadin abubuwan da muka sani, kuma muna shaida abubuwan da muka gani. Duk da haka ba ku karbi shaidar mu ba.
12Idan na gaya maka abubuwan da ke na duniya amma baka gaskata ba, to yaya zaka gaskata idan na gaya maka abubuwa na sama?
13Babu wanda ya taba hawa zuwa sama sai dai shi wanda ya sauko daga sama: wato Dan Mutum.
14Kamar yadda Musa ya ta da maciji a jeji, haka ma dole a ta da Dan Mutum

Read Yahaya 3Yahaya 3
Compare Yahaya 3:3-14Yahaya 3:3-14