Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Yahaya - Yahaya 2

Yahaya 2:4-16

Help us?
Click on verse(s) to share them!
4Yesu yace mata, “Mace, me yasa kika zo wurina? Lokaci na bai yi ba tukuna”.
5Maihafiyarsa tace wa ma'aikatan, “Ku yi duk abin da yace maku.”
6To akwai randunan ruwa na dutse guda shidda a wurin wadanda Yahudawa ke amfani da su domin al'adansu na tsarkakewa, kowace zata iya daukar durom guda.
7Yesu yace masu, “Cika randunan da ruwa”. Sai suka cika randunan makil.
8Sai yace wa ma'aikatan, “Ku diba daga ciki ku kai wa shugaban biki.” Sai suka yi hakannan.
9Shugaban bikin ya dandana ruwan da ya zama ruwan inabin, amma bai san inda ya fito ba (amma ma'aikatan wadanda suka jawo ruwan sun sani). Sai ya kira ango
10yace masa, “Kowane mutum yakan raba ruwan inabi mai kyau da farko, kafin mai arhar bayan an shanye mai kyaun. Amma kai ka ajiye mai kyaun sai yanzu.”
11Wannan alama ta farko ce da Yesu yayi a Kana ta Galili, ya kuma bayyana daukakarsa, almajiransa kuma suka gaskata da shi.
12Bayan wannan, Yesu, da mahaifiyarsa, da 'yan'uwansa da almajiransa suka tafi Kafarnahum, kuma suka zauna can wasu 'yan kwanaki.
13To idin ketarewa na Yahudawa ya kusato, Yesu kuwa ya wuce zuwa Urushalima.
14Ya iske wadanda suke sayar da shanu da tumaki da tantabaru, masu canjin kudi kuma na zaune a wurin.
15Sai yayi tsumingiya da igiyoyi ya kore su duka daga cikin haikalin, duk da tumakin da shanun. Sai ya watsar da sulallan masu canjin kudin ya birkitar da teburansu.
16Yace wa masu sayar da tantabaru, “Ku fitar da wadannan abubuwa daga nan. Ku daina maida gidan Ubana wurin kasuwanci.”

Read Yahaya 2Yahaya 2
Compare Yahaya 2:4-16Yahaya 2:4-16