Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Yahaya - Yahaya 2

Yahaya 2:15-23

Help us?
Click on verse(s) to share them!
15Sai yayi tsumingiya da igiyoyi ya kore su duka daga cikin haikalin, duk da tumakin da shanun. Sai ya watsar da sulallan masu canjin kudin ya birkitar da teburansu.
16Yace wa masu sayar da tantabaru, “Ku fitar da wadannan abubuwa daga nan. Ku daina maida gidan Ubana wurin kasuwanci.”
17Almajiransa suka tuna a rubuce yake, “Himma domin gidanka za ta cinye ni.”
18Sai shugabannin Yahudawa suka amsa suka ce masa, “Wace alama za ka nuna mana, da shike kana yin wadannan abubuwan?”
19Yesu ya amsa, “Ku rushe wannan haikali, kuma a cikin kwana uku zan gina shi.”
20Sai shugabanin Yahudawa suka ce, “An dauki shekaru arba'in da shidda kamin a gama gina wannan haikalin, za ka dau kwanaki uku kadai wajen gina shi?”
21Amma yana nufin haikali na jikinsa ne.
22Bayan da aka tashe shi daga matattu, sai almajiransa suka tuna ya fadi haka, suka kuma ba da gaskiya ga nassi da wannan kalami da Yesu ya fada.
23Kuma, da yana Urushalima a idin ketarewa, a lokacin idin, mutane da yawa suka gaskata ga sunansa, sa'adda suka ga alamun da ya yi.

Read Yahaya 2Yahaya 2
Compare Yahaya 2:15-23Yahaya 2:15-23