Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Yahaya - Yahaya 21

Yahaya 21:8-24

Help us?
Click on verse(s) to share them!
8Sauran almajiran kuwa suka zo a cikin karamin jirgi, (domin basu da nisa da kasa, kamar kamu dari biyu zuwa sama), janye da tarun cike da kifi.
9Da isowarsu gaci, sai suka ga garwashin wuta a wurin da kifi akai, da kuma gurasa.
10Yesu ya ce masu “Ku kawo wandansu daga cikin kifin da kuka kama yanzu”.
11Sai Saminu Bitrus ya hau, ya jawo tarun gaci, cike da manyan kifaye dari da hamsin da uku (153). Amma duk da yawansu, tarun bai tsage ba.
12Yesu yace masu, “Ku zo ku karya kumallo”. Daga cikin almajiran kuwa babu wanda yayi karfin halin tambayarsa “Ko shi wanene?” Domin sunsani Ubangiji ne.
13Yesu zo ya dauki gurasar ya ba su, haka kuma kifin.
14Wannan shine karo na uku da Yesu ya bayyana ga almajiransa bayan tashinsa daga matattu.
15Da suka karya kumallon, Yesu yace wa Saminu Bitrus, “Bitrus dan Yahaya, kana kaunata fiye da wadannan?” Bitrus yace masa “I ya Ubangiji, ka sani ina kaunarka” Yesu yace masa “Ka ciyar da 'ya'yan tumakina”.
16Ya sake fada masa karo na biyu, “Saminu Dan Yahaya, kana kaunata?” Bitrus Yace masa “I ya Ubangiji, ka sani ina kaunarka”. Yesu yace masa, “Ka lura da Tumakina”.
17Ya sake fada masa, karo na uku, “Bitrus Dan Yahaya, kana kaunata? Sai Bitrus bai ji dadi ba domin Yesu ya fada masa karo na uku, “Kana kaunata” Yace masa, “Ubangiji ka san komai duka, ka sani ina kaunarka.” Yesu yace masa “Ka ciyar da tumaki na.
18Hakika, hakika, Ina gaya maka, lokacin da kake kuruciyarka, kakan yi wa kanka damara, ka tafi inda ka ga dama. amma in ka tsufa, zaka mike hannuwanka wani yayi maka damara, ya kai ka inda baka nufa ba.”
19To Yesu ya fadi haka ne domin ya nuna irin mutuwar da Bitrus zai yi ga daukakar Allah. Bayan ya fadi haka, sai yace wa Bitrus, ka biyo ni.
20Bitrus ya juya sai ya ga almajirin da Yesu yake kauna yana biye dasu; wanda ya jingina a kirgin Yesu lokacin cin jibin nan da yace “Ya Ubangiji, wanene zai bashe ka?”
21Da Bitrus ya gan shi, yace wa Yesu “Ya Ubangiji, Me mutumin nan zai yi?”
22Yesu yace masa, “Idan ina so ya zauna har in dawo ina ruwanka? Ka biyo ni.”
23Wannan zance ya yadu cikin 'yan'uwa cewa, wannan almajirin ba zai mutu ba. Alhali Yesu bai cewa Bitrus, wannan almajirin ba zai mutu ba, Amma “Idan ina so ya zauna har in dawo ina ruwanka?”
24Wannan shine almajirin da yake shaida wadannan abubuwa, wanda ya rubuta su, kuma mun tabbata shaidarsa gaskiya ne.

Read Yahaya 21Yahaya 21
Compare Yahaya 21:8-24Yahaya 21:8-24