Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Yahaya - Yahaya 11

Yahaya 11:29-44

Help us?
Click on verse(s) to share them!
29Da ta ji haka, sai ta tashi da sauri ta tafi wurin sa.
30Yesu bai rigaya ya shiga kauyen ba, yana nan inda Matta ta zo ta same shi.
31Da Yahudawan nan dake tare da Maryamu, wato wadannan da suka zo mata ta'aziya, suka ga ta fita daga chikin gida da sauri, sai suka bi ta, suna tsammanin cewa ta tafi ta yi kuka ne a kabari.
32Da Maryamu ta kai inda Yesu ya ke, sai ta fadi gaban sawayensa, ta ce, “Ubangiji, inda kana tare da mu, da dan'uwana bai mutu ba”.
33Da Yesu ya gan ta tana kuka, da wadannan Yahudawa da suka bi ta, sai ya yi juyayi a ruhu ya damu kuma;
34sai ya ce, “A ina kuka kwantar da shi?” Sai suka ce masa, “Ubangiji, zo ka gani.”
35Yesu ya yi kuka.
36Sai Yahudawa suka ce, “Dubi yadda yake kaunar Li'azaru!”
37Amma wadansun su suka ce, “Shi wannan mutum da ya iya ba makaho ganin gari, da bai iya hana wannan mutum mutuwa ba?
38Yesu yana cikin juyayi kuma a cikin kansa, sai ya tafi kabarin. Kabarin a kogo ne an kuma rufe bakinsa da dutse.
39Sai Yesu ya ce, “A kawar da dutsen.” Matta yar'uwar Li'azaru wanda ya mutu, ta ce wa Yesu, “Ubangiji, Yanzu jikin ya ruba domin ya kai kwana hudu da mutuwa”.
40Yesu ya ce mata, “Ba na ce maki idan kin gaskata za ki ga daukakar Allah ba?”
41Sai suka kawar da dutsen. Yesu ya daga idanunsa ya ce, “Uba, na gode maka domin kana ji na.”
42Na san kana ji na a kowane lokaci, amma domin wannan taro da ke tsaye kewaye da ni nike wannan magana, domin su bada gaskiya cewa kaine ka aiko ni.”
43Bayan ya yi wannan magana, sai ya daga murya ya ce, “Li'azaru, ka fito!”
44Sai mataccen ya fito; kafafunsa da hannayensa na daure da likkafani, fuskarsa kuma na lullube da tsumma. Yesu ya ce masu, “Ku kwance shi, ya tafi”.

Read Yahaya 11Yahaya 11
Compare Yahaya 11:29-44Yahaya 11:29-44