Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Romawa - Romawa 7

Romawa 7:8-19

Help us?
Click on verse(s) to share them!
8Amma zunubi, sai ya dauki zarafi ta wurin dokar, ya jawo dukkan sha'awa dake cikina. Domin in da babu shari'a, zunubi matacce ne.
9Ada na rayu sau daya ba tare da shari'a ba, amma da dokar ta zo, sai zunubi ya farfado, ni kuma na mutu.
10Dokar wadda ta kamata ta kawo rai, sai na same ta matacciya.
11Domin zunubin, ya dauki zarafi ta wurin dokar, ya rude ni, kuma ta wurin dokar ya kashe ni.
12Domin haka, shari'ar na da tsarki, dokar na da tsarki, adalci da kuma kyau.
13To abu mai kyau ya zamar mani mutuwa kenan? ba zai taba zama haka ba. Amma zunubi, domin ya nuna shi zunubi ne ta wurin abin da ke mai kyau, sai ya kawo mutuwa a cikina. Wannan ya kasance haka ne domin ta wurin dokar, zunubi ya zama cikakken zunubi.
14Domin mun san shari'a mai Ruhaniya ce, amma ni ina cikin jiki. An sai da ni karkashin bautar zunubi.
15Domin ni ma ban fahimci abin da nake aikatawa ba. Domin abin da nake so in aikata, ba shi nake aikatawa ba, kuma abin da bana so, shi nake aikatawa.
16Amma idan na aikata abin da bana so, na amince da shari'a kenan, cewar shari'a nada kyau.
17Amma yanzu ba ni ke aikata abin ba, amma zunubi da ke zaune a cikina.
18Domin na san a cikina, wato cikin jikina, babu wani abu mai kyau. Domin marmarin aikata abu mai kyau na tare da ni, amma ba ni iya aikatawa.
19Domin abu mai kyau da na ke so in aikata bana iyawa, amma muguntar da ba na so ita na ke aikatawa.

Read Romawa 7Romawa 7
Compare Romawa 7:8-19Romawa 7:8-19