Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Romawa - Romawa 2

Romawa 2:1-22

Help us?
Click on verse(s) to share them!
1Saboda da haka baka da hujja, kai mutum, kai mai shara'antawa, domin kuwa abinda kake shara'antawa akan wasu kana kada kanka da kanka. Domin kuwa kai mai shar'antaawa kana aikata wadannan abubuwa.
2Amma mun san cewa shari'ar Allah ta gaskiya ce sa'adda zata fado wa masu aikata wadannan irin abubuwa.
3Amma ka lura da wannan, ya kai mutum, mai shara'anta masu aikata wadannan ababuwa. Duk da shike kaima kana aikatawa. Kana jin zaka kubucewa hukuncin Allah?
4Ko kana raina falalar alheransa da yake yi ta wajen jinkirin hukuncinsa, da hakurinsa? Baka san cewa alheransa musanman domin su kai ka ga tuba bane?
5Amma saboda taurin kanka da zuciyarka marar tuba, kana tanadarwa kanka fushi, a ranar fushi, wato ranar bayyanuwar shari'ar adalci ta Allah.
6Zai baiwa kowanne mutum daidai sakamakon ayyukansa:
7Ga wadanda kuma suka nace da yin ayyukan alheri ba fasawa, sun samarwa kansu, yabo da daraja, da rai na har'abada.
8Amma ga masu son kai, wadanda suka ki yin biyayya ga gaskiya, suka yiwa rashin adalci biyayya, fushi da hasala mai zafi zai afko masu.
9Allah kuma zai sauko da bala'i da bakin ciki ga dukkan rayukan da suka aikata mugunta, ga Yahudawa da fari, sannan kuma Hellinawa.
10Amma yabo daraja da salama zasu kasance ga dukkan wadanda suka aikata ayukan alheri, ga Yahudawa da fari sannan Hellanawa.
11Domin kuwa Allah ba mai tara bane.
12Ga wadanda suka yi zunubi batare da shari'aba, zasu hallaka ba tare da shari'a ba, ga wadanda suka yi zunubi cikin shari'a kuma za'a hukunta su bisa ga shari'a.
13Domin kuwa ba masu jin shari'ar ne masu adalci agaban Allah ba, amma masu aikatawa ne zasu samu barata.
14Gama al'umai da basu san shari'a ba, bisa ga dabi'a sun yi abinda ke na shari'a, sun kuma zame wa kansu shari'a, koda shike basu da shari'ar.
15Dalilin haka kuwa sun nuna cewa ayukan da shari'a take bukata na nan a rubuce a zuciyarsu. lamirinsu kuma na yi masu shaida, tunanainsu kuma, ko dai yana kashe su, ko kuma yana karesu.
16hakanan kuma ga Allah. Wannan zai faru ranar da Allah zai shara'anta asiran boye na dukkan mutane, bisa ga bishara ta cikin Yesu Almasihu.
17Da shike kana kiran kanka Bayahude, kana zaune akan shari'a, kana alfahari cikin Allah,
18ka san nufinsa, ka kuma san abubuwan da suka bambanta da hakan, ka kuma sami koyarwa cikin shari'ar.
19Da shike kana da gabagadi akan cewa kai jagora ne ga makafi, haske ga wadanda suke cikin duhu,
20mai horo ga marasa hikima, mai koyar da jarirai, kuma a cikin shari'ar kana da abin da ya shafi sani da kuma gaskiya.
21ku da kuke koyar da wadansu, ba ku koyar da kanku? ku da kuke wa'azi kada ayi sata, ba ku yin sata?
22Ku da ke wa'azi kada ayi zina, ba ku yin zina? ku da ke hana bautar gumaka, ba ku yin sata a haikali?

Read Romawa 2Romawa 2
Compare Romawa 2:1-22Romawa 2:1-22