Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Romawa - Romawa 1

Romawa 1:16-28

Help us?
Click on verse(s) to share them!
16Don kuwa ni ba na jin kunyar yin bishara, don ita ce ikon Allah don samun ceto ga duk wanda ya gaskata, da farko dai Yahudawa kana kuma Hellinawa,
17Domin a cikin ta adalcin Allah ya bayyana daga bangaskiy zuwa bangaskiya, kamar yadda yake a rubuce, “Mai adalci zai rayu ne tawurin bangaskiya.”
18Domin fushin Allah ya bayyana ne daga sama gaba da rashin ibada da rashin adalci na yan'adam, wadanda suke danne gaskiya ta wurin rashin adalcin su.
19Dalili kuwa abinda yakamata a sani game da Allah a bayyane ya ke a gare su. Domin kuwa Allah ya bayyana masu shi a zahiri.
20Domin al'amuransa da ba'a iya gani a bayyane suke tun halittar duniya. A na iya gane su ta wurin halitatattun abubuwa. Wadannan al'amura kuwa sune madawwamin ikonsa da Allahntakarsa. Sakamakon haka, wadannan mutane ba su da hujja.
21Dalili kuwa, koda suna jin sun san Allah, amma basu darajanta shi a matsayin Allah ba, ko kuma su nuna masa godiya. Maimakon haka, suka zama wawaye a cikin tunaninsu, zukatansu marasa tunani sun duhunta.
22Suna daukar kansu akan masu hikima ne su, amma sai ga su sun zama wawaye.
23Sun musanya daukakar Allah madawwami da ta kamannin abubuwan da basa dawwama, kamar mutum, da tsuntsaye, da dabbobi masu kafafu hurhudu, da masu jan ciki.
24Saboda haka Allah ya bashe su ga sha'awoyin kazantar zukatansu, su wulakantar da jukunansu a junansu.
25Sune suka musanya gaskiyar Allah da karya, Kuma suke sujada da bauta ga halittaccen abu, maimakon Mahaliccin, Wanda yake abin yabo har abada. Amin.
26Saboda haka Allah ya bashe su, ga sha'awowin su na lalata da wulakanci, har matansu suka canza ka'idar jima'i da aka saba zuwa madigo mace da mace.
27Mazajensu ma suka sauya ka'idar jima'i tsakanin mace da miji zuwa namiji da namiji suna yin aikin lalata. Maza su na kwana da maza suna aikata aikin ban kyama, suna kuwa girbe sakamakon aiknsu na ban kyama.
28Tunda shike ba su amince da Allah a cikkin al'amuransu ba, Allah ya bashe su ga bataccen hankalinsu, su aikata wadannan munanan abubuwa.

Read Romawa 1Romawa 1
Compare Romawa 1:16-28Romawa 1:16-28