Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Romawa - Romawa 15

Romawa 15:3-19

Help us?
Click on verse(s) to share them!
3Domin Almasihu bai faranta wa kansa rai ba. Kamar yadda aka rubuta, “zagin da wadansu suka yi masa ya sauka a kaina.”
4Don abin da aka rubuta a baya an rubuta ne domin a gargade mu, domin ta hakuri da karfafawar litattafai mu sami karfi.
5Yanzu Allah mai hakuri da karfafawa ya baku zuciya daya ta zaman tare da juna bisa ga halin Yesu Almasihu.
6Domin ya yi haka ne da zuciya daya domin ku yi yabo da bakinku daya.
7Domin ku karbi juna, kamar yadda Yesu ma ya karbe ku domin a daukaka Allah.
8Saboda na ce an mai da Almasihu bawan kaciya a madadin gaskiyar Allah. Ya yi wannan ne don a tabbatar da alkawarai da aka ba kakanin kakaninmu.
9Domin Al'umai su daukaka Allah saboda jinkansa, kamar yadda ya ke a arubuce, “Domin ta haka zan yabe ka cikin Al'umai in yi wakar yabon sunanka.”
10Kuma an ce. “Ku yi faranciki, ku Al'ummai tare da mutanensa.”
11Kuma.” Ku yabi Ubangiji, ku dukan Al'ummai; bari dukan mutane su yabe shi.”
12Kuma, Ishaya ya ce “Za a sami tsatson Yessi, wanda zai tashi ya yi mulki a kan Al'umai, Al'umai za su sami karfin hali a cikinsa.”
13Yanzu Allah mai karfafawa ya cika ku da dukkan farin ciki salama, saboda da bangaskiyarku, domin ku sami cikkakiyar karafafawa, ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki.
14Ni kaina na amince da ku, yan'uwa. Kuma na amince cewa ku da kanku kuna cike da alheri, cike da dukkan sani. Na amince cewa za ku sami zarafi ku gargadi juna.
15Amma ina rubuta maku da gabagadi kan wadansu abubuwa, domin in tunasheku, saboda baiwar da aka bani daga wurin Allah.
16Cewa baiwar ta sa na zama bawan Almasihu Yesu da aka aika ga Al'ummai, limami na bisharar Allah. Zan yi wannan saboda baikon Al'ummai ya zama karbabbe, kuma kebbabe ga Allah ta wurin Ruhu Mai Tsarki.
17Don haka ina jin dadi cikin Yesu Almasihu da abubuwa na Allah.
18Domin ba ni da abin da zan ce, sai abin da Yesu ya aikata ta wurina, domin Al'ummai su yi biyayya ta magana da aiki.
19Ta wurin alamu, da al'jibai, da ikon Ruhu Mai Tsarki. Daga Urushalima, da kewaye har zuwa Ilirikum, an kai bisharar Almasihu ko'ina dukka.

Read Romawa 15Romawa 15
Compare Romawa 15:3-19Romawa 15:3-19