Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Romawa - Romawa 14

Romawa 14:14-20

Help us?
Click on verse(s) to share them!
14Na sani na kuma tabbata tsakani na da Ubangiji Yesu, ba abin da yake mara tsarki ga asalinsa. Sai dai ga wanda ya dauke shi marar tsarki ne yake zama marar tsarki.
15Idan har abincinka na cutar da dan'uwanka, ba ka tafiya cikin kauna. Kada ka lalata wanda Yesu ya mutu domin sa da abincinka.
16Saboda haka, kada abubuwan da aka dauka kyawawa su zama abin zargi ga wadansu.
17Saboda mulkin Allah ba maganar ci da sha ba ne, amma game da adalci ne, salama, da farin ciki a cikin Ruhu Mai Tsarki.
18Domin wanda yake bautar Almasihu a wannan hanya, karbabbe ne ga Allah, kuma jama'a sun yarda da shi.
19Don haka, mu nemi abubuwa na salama da abubuwan da zasu gina juna.
20Kada ku lalata aikin Allah don abinci. Komai yana da tsarki, amma kaiton mutumin da yake cin abin da zai sa shi ya fadi.

Read Romawa 14Romawa 14
Compare Romawa 14:14-20Romawa 14:14-20