Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Romawa - Romawa 12

Romawa 12:2-8

Help us?
Click on verse(s) to share them!
2Kada ku kamantu da wannan duniya, amma ku sami canzawa ta wurin sabunta tunaninku, kuyi haka don ku san abin da ke nagari, karbabbe, kuma cikakken nufin Allah.
3Don ina cewa, saboda alherin da aka bani, ka da waninku ya daukaka kansa fiye da inda Allah ya ajiye shi; a maimakon haka ku kasance da hikima, gwargwadon yadda Allah yaba kowa bangaskiya.
4Domin muna da gababuwa da yawa a jiki daya, amma ba dukansu ne ke yin aiki iri daya ba.
5haka yake a garemu, kamar yadda muke da yawa haka cikin jikin Almasihu, dukkanmu gabobin juna ne.
6Muna da baye-baye dabam-dabam bisa ga alherin da aka bayar a gare mu. Idan baiwar wani anabci ne, yayi shi bisa ga iyakar bangaskiyarsa.
7In wani yana da baiwar hidima, sai yayi hidimarsa. Idan baiwar wani koyarwa ce, yayi koyarwa.
8Idan baiwar wani karfafawa ce, yayi ta karfafawa; Idan baiwar wani bayarwa ce, yayi ta da hannu sake; Idan baiwar wani shugabanci ne, yayi shi da kula; Idan baiwar wani nuna jinkai ne, yayi shi da sakakkiyar zuciya.

Read Romawa 12Romawa 12
Compare Romawa 12:2-8Romawa 12:2-8