Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Romawa - Romawa 11

Romawa 11:1-22

Help us?
Click on verse(s) to share them!
1Sai na ce, Allah ya ki mutanensa ne? Ba zai taba yiwuwa ba. Domin ni ma ba-Isra'ile ne, na zuriyar Ibrahim, a kabilar Bilyaminu.
2Allah bai ki mutanen sa da ya ke da rigyasaninsu ba. Ko kun san abin da nassi ya ce game da Iliya, yadda ya kai karar Isra'ila a gaban Allah?
3Ya ce, “Ubangiji, sun kashe annabawanka, sun rushe alfarwanka kuma, Ni kadai ne na rage, ga shi suna neman su kashe ni.”
4Amma wacce amsa ce Allah ya ba shi? Ya ce, “Ina da mutane dubu bakwai da na kebe don kaina, da ba su taba rusuna wa Ba'al ba.”
5Ban da haka ma, ban da haka ma a wannan lokacin akwai sauran zabe na alheri.
6Amma tun da ta wurin alheri ne, ba ga ayyuka ba. In ba haka ba, alheri ba zai zama alheri ba kenan.
7Sai kuma me? Abin da Isra'ila ke nema, ba su samu ba, amma zababbun sun same shi, saura kuma sun taurare.
8Kamar yadda yake a rubuce, “Allah ya ba su ruhun rashin fahimta, ga idanu amma ba za su gani ba, ga kunnuwa amma ba za su ji ba, har zuwa wannan rana.”
9Dauda kuma ya ce, “bari teburinsu ya zama taru, da tarko, ya zama dutsen tuntube da abin ramako a gare su.
10Bari idanunsu ya duhunta domin kada su gani; bayansu kuma a duke kullum.”
11Na ce, “sun yi tuntube domin su fadi ne?” Kada abu kamar haka ya faru. A maimakon haka, juyawa baya da suka yi ya sa, ceto ya zo ga Al'ummai, domin ya sa su kishi.
12Idan yanzu juyawa baya da sun yi ya zama arziki ga duniya, rashin su kuma arziki ga Al'ummai, yaya kwatancin girmansa zai kasance in sun zo ga kammala?
13Yanzu ina magana da ku ku da ke Al'ummai. Tunda yake ni ne manzo ga Al'ummai, ina kuma fahariya cikin hidimata.
14Yana yiwuwa in sa “yan'uwa na kishi, domin mu ceci wadansu su.
15Idan kinsu ya kawo sulhuntawa ga duniya, Karbarsu kuma zata zama yaya? Zata zama rai ne daga mutuwa.
16'ya'yan farko sunan haka ma kakkabensu yake, Idan saiwar itace na nan, haka ma rassan za su zama.
17Amma idan an karye wasu daga cikin rassan, idan ku rassan zaitun na ainihi ne, da aka samu daga cinkinsu, kuma idan kuna da gado tare da su, acikin saiwar itacen zaitun din.
18Kada ku yi fahariya a kan rassan. Amma idan kuka yi fahariya to ba ku bane masu karfafa saiwar amma saiwar ce ke karfafa ku.
19Kana iya cewa, “An karye rassan domin a same ni a ciki.”
20Wannan gaskiya ne! Saboda rashin bangaskiyarsu ne ya sa aka karye su daga rassan, amma ku tsaya da karfi acikin bangaskiyarku. Kada ku dauki kanku fiye da yadda ya kamata, amma ku ji tsoro.
21Domin idan Allah bai bar ainihin rassan ba, to ba zai bar ku ba.
22Ku duba yadda irin ayyuka masu tsananni na Allah. Ta daya hannun kuma, tsanannin kan zoa kan Yahudawa wadanda suka fadi. Har 'ila yau jinkai Allah ya zo maku, idan kun cigaba cikin alherinsa baza a sare ku ba. Amma in kun ki za a sare ku.

Read Romawa 11Romawa 11
Compare Romawa 11:1-22Romawa 11:1-22