Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Romawa - Romawa 10

Romawa 10:4-14

Help us?
Click on verse(s) to share them!
4Gama Almasihu shi ne cikar doka zuwa ga adalci ga dukkan wadanda suka gaskata.
5Musa kam ya rubuta game da adalci da zai samu ta shari'a: “mutumin da ya aikata adalcin shari'a, zai rayu ta wurin wannan adalcin.”
6Amma adalcin da ya zo ta wurin bangaskiya yace, “Kada ku ce a zuciyarku, wa zai hau zuwa sama?” (don ya sauko da Almasihu kasa).
7Kada ku ce, “Wa zai gangara zuwa kasa?” (Wato wa zai fito da Almasihu daga cikin matattu).
8Amma me yake cewa? “kalmar tana kusa da kai a cikin bakinka da kuma cikin zuciyarka.” Wato kalmar bangaskiya, wadda muke shaidawa.
9Don idan da bakinka, ka shaida Yesu Ubangiji ne, kuma ka gaskata a zuciyarka cewa Allah ya tashe shi daga matattu, za ka sami ceto.
10Don da zuciya ne mutum yake gaskatawa zuwa ga adalci, da kuma baki ne yake shaida zuwa ga ceto.
11Don nassi na cewa, “Duk wanda ya gaskata da shi ba zai ji kunya ba,”
12Gama ba bambanci tsakanin Bayahude da Ba'al'ume. Gama dukkansu Ubangijinsu daya ne, Shi mayalwaci ne ga dukkan wanda ya kira shi.
13Duk wanda ya kira sunan Ubangiji zai sami ceto.
14To ta yaya zasu kira ga wanda basu gaskata ba? Kuma ta yaya zasu gaskata ga wanda ba su taba jin labarinsa ba?

Read Romawa 10Romawa 10
Compare Romawa 10:4-14Romawa 10:4-14