Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Romawa - Romawa 10

Romawa 10:10-21

Help us?
Click on verse(s) to share them!
10Don da zuciya ne mutum yake gaskatawa zuwa ga adalci, da kuma baki ne yake shaida zuwa ga ceto.
11Don nassi na cewa, “Duk wanda ya gaskata da shi ba zai ji kunya ba,”
12Gama ba bambanci tsakanin Bayahude da Ba'al'ume. Gama dukkansu Ubangijinsu daya ne, Shi mayalwaci ne ga dukkan wanda ya kira shi.
13Duk wanda ya kira sunan Ubangiji zai sami ceto.
14To ta yaya zasu kira ga wanda basu gaskata ba? Kuma ta yaya zasu gaskata ga wanda ba su taba jin labarinsa ba?
15Kuma ta yaya zasu ji in ba ayi masu wa'azi ba? Kuma ta yaya zasu yi wa'azin in ba an aike su ba? - Kamar yadda yake a rubuce, “Ina misalin kyau na kafafun wadanda ke shaida labarin farin ciki na abubuwa masu kyau!”
16Amma ba dukkansu ne suka ji bishara ba. Gama Ishaya ya ce, “Ubangiji, wa ya gaskata da sakon?
17Saboda haka bangaskiya na zuwa ta wurin ji, jin kuwa daga maganar Almasihu.
18Amma na ce, “ko basu ji ba ne? I, tabbas” muryarsu ta kai dukkan duniya, kuma kalmominsu sun kai har karshen duniya.”
19yau, na ce, “Ko Isra'ila basu sani ba ne?” Da farko Musa ya ce, “Zan sa kuyi fushi da kishi da abin da ba al'umma ba. Abin da nake nufi nan shine al'ummar da basu da fahinta, zan more su, in tayar maku da hankali.”
20Amma Ishaya da karfin hali ya ce, “Ga wadanda basu neme ni ba suka same ni. Na bayyana ga wadanda basu nemi ni ba.
21“Amma ga Isra'ila kam ya ce, “na mika hannu na ga masu rashin biyayya dukkan tsawon rana, domin su mutane ne masu taurin kai.”

Read Romawa 10Romawa 10
Compare Romawa 10:10-21Romawa 10:10-21