Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Markus - Markus 7

Markus 7:2-17

Help us?
Click on verse(s) to share them!
2Sun ga cewa wasu daga cikin almajiransa sun ci gurasa da hannuwa marasa tsabta, wato, basu wanke hannu ba,
3(Domin Farisawa da dukan Yahudawa ba su cin abinci sai dole sun wanke hannu da kyau domin suna kiyaye al'adun dattawa.
4Idan Farisawa suka dawo daga kasuwa, wajibi ne su yi wanka kamin su ci abinci. Akwai sauran al'adun da suke kiyayewa, kamar wanke moda, tukwane, da wasu santula na dalma, har da dakin cin abinci.)
5Farisawa da Marubuta suka tambaye Yesu, “Don me almajiran ka basu kiyaye al'adun dattawa, domin suna cin abinci ba tare da sun wanke hannu ba?”
6Amma ya amsa masu cewa, “Ishaya ya yi anabci akan ku masu bautan ganin ido, da ya rubuta cewa 'wadanan mutane suna girmama ni a baka amma zuciyar su tana nesa da ni.
7Sujadar wofi suke mani suna koyar da ka'idodi na mutane a matsayin rukunansu'”.
8Kun watsar da dokar Allah sai kuka rungumi al'adun mutane.
9Sai yace masu, kun yi nasara wurin kau da dokokin Allah domin ku kiyaye al'adun ku na mutane.
10Koda shike Musa ya rubuta cewa, “ka girmama Ubanka da Uwarka”, kuma, “duk wanda ya zagi Ubansa ko Uwatasa, ya cancanci mutuwa nan take”.
11Amma kun ce, 'idan mutum ya ce wa iyayensa, “duk taimakon da ya cacanci ku samu daga guna ya zama kebabbe (wato, 'na mika wa Allah)”'.
12Sabo da haka, kun ba shi izini kada ya yi wa Ubansa ko Uwatasa wani abu.
13Kuna mayar da dokan Allah abin banza, sabili da al'adun ku da kuka mika masu. Wannan, da wasu abubuwa kamar haka kuke yi.”
14Ya kara kiran taron jama'ar yace masu, “ku kasa kunne gareni, kuma ku gane.
15Babu wani abu daga wajen mutum da zai iya gurbatar da shi har idan ya shiga cikinsa. Amma, abinda ya fita daga cikinsa shike gurbatar da shi”
16Bari mai kunnen ji, ya ji.
17Da Yesu ya bar taron jama'ar, ya shiga gida, sai almajiransa suka tambaye shi ma'anar wannan misali.

Read Markus 7Markus 7
Compare Markus 7:2-17Markus 7:2-17