Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Luka - Luka 8

Luka 8:30-38

Help us?
Click on verse(s) to share them!
30Sa'annan Yesu ya tambaye shi, “Yaya sunanka?” Sai ya ba da amsa, “Suna na dubbai.” Ya ce haka ne domin aljanu da yawa sun shiga wannan mutum.
31Aljanun suka yi ta rokon Yesu kada ya ummarce su su shiga cikin rami mai zurfi.
32Akwai babban garken aladu su na kiwo a kan tsauni kusa da wurin. Aljanun suka roki Yesu da ya barsu su shiga cikin aladun, shi kuwa ya yarda masu.
33Aljanun suka bar mutumin suka shiga cikin aladun, sai garken aladun suka gangara kwari suka fada cikin tafkin, suka nutse.
34Lokacin da mutanen da su ke kiwon aladun suka ga abin da ya faru, sai suka gudu! Suka ba da rahoton abin da ya faru ga mutanen cikin gari da na wannan kewayen.
35Don haka, mutanen da suka ji haka suka tafi domin su ga abin da ya faru, suka zo wurin da Yesu yake, suka ga mutumin wanda aljanu suka fita daga cikinsa. Suka ga ya na sanye da tufafi, kuma ya na cikin hankalinsa, sai tsoro ya kama su.
36Mutanen da suka ga abin da ya faru, suka gaya wa wadansu yadda aka warkar da mutumin da aljanu suke iko da shi.
37Sai dukan mutane wadanda suke cikin yankin Garasinawa da wadanda suke kewaye, suka roki Yesu da ya fita daga cikin yankin kasarsu domin sun ji tsoro kwarai da gaske. Daga nan Yesu da almajiransa suka shiga cikin jirgin ruwa suka koma.
38Mutumin wanda aljanu suka fita daga cikinsa, ya roki Yesu cewa, “Ka barni in tafi tare da kai!” Amma Yesu ya sallame shi cewa,

Read Luka 8Luka 8
Compare Luka 8:30-38Luka 8:30-38