Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Luka - Luka 8

Luka 8:14-36

Help us?
Click on verse(s) to share them!
14Irin da suka fada cikin kayayuwa, sune mutanen da suka ji maganar, amma da suka ci gaba da rayuwa, sai suka bari matsalolin rayuwa kamar dukiya da jin dadin rayuwa suka fi karfinsu, sai ya zama ba su iya bada 'ya'yan da suka yi girma ba.
15Amma irin da suka fada a kan kasa mai kyau, wadannan sune mutanen da suka ji maganar, suka karbe ta da gaskiya da zuciya daya, sun rike ta kam-kam, suna jimrewa wurin ba da 'ya'ya.
16Ba mai kunna fitila, ya rufe ta da kasko, ko su sa ta a karkashin gado. Amma sai a sa ta a wurin zaman ta domin duk wanda ya shigo ya iya ganin hasken ta.
17Babu abin da yake a boye wanda ba za a tone shi ba, ko wani asiri da ba za ya fito fili a san shi ba.
18Ku yi hankali da yadda kuke ji, domin duk mai abu, shi za a kara wa, kuma duk mara abu, dan kadan da yake tunani yana da shi ma, za a dauke.”
19Sai mahafiyar Yesu da 'yan'uwansa, su ka zo wurinsa, amma ba su iya zuwa ko kusa da shi ba saboda taron jama'a.
20Sai wani ya gaya masa, “Ga mahaifiyarka da 'yan'uwanka, su na tsayuwa a waje, su na son ganin ka.”
21Amma Yesu ya amsa ya ce ma su, “Mahaifiyata da 'yan'uwana sune wadanda suke jin maganar Allah, suke yin biyayya da ita.”
22Wata rana kuma Yesu ya shiga cikin jirgin ruwa, shi da almajiransa. Ya ce masu, “Ina so mu je dayan ketaren tafkin.” Sai su ka fara tafiya domin su ketare tafkin.
23Amma sa'adda su ke tafiya sai Yesu ya yi barci, sai wata iska mai karfi ta taso cikin tafkin, nan da nan sai jirgin ya fara cika da ruwa, kuma su na cikin hatsari.
24Sai almajiran Yesu su ka zo su ka tashe shi daga barci. Suka ce da shi, “Ya Shugaba! Ya Shugaba! Za mu mutu!” Sai ya tashi ya umarci iskar, sai iskar mai hauka da tumbatsar ruwan sun tsaya tsit.
25Daga nan sai ya ce da su, “Ina bangaskiyar ku?” Almajiran suka tsorata suka yi mamakin abin da ya faru nan take. Suka ce wa junansu, “Wanene wannan wanda har zai ba iska da ruwa umarni kuma su yi masa biyayya?”
26Suka zo yankin Garasinawa, wanda ke kusa da Gallili.
27Sa'adda Yesu ya sauka kasa, sai wani mutum daga wannan yankin ya tarbe shi. Wannan mutum kuwa yana da aljanu. Mutumin ya dade ba ya sa tufafi, kuma ba ya zama a gida. Maimakon haka, sai a cikin kabarbura ya ke zama.
28Sa'adda ya ga Yesu, mutumin ya yi ihu da karfi, ya rusuna a gabansa da babban murya ya ce, “Me zan yi da kai, Yesu, Dan Allah Madaukaki? Ina rokonka, kada ka ba ni azaba!”
29Domin Yesu ya umarci aljanun su fita daga cikinsa, domin sau da dama aljanun sukan kama shi. Ko an daure mutumin da sarkoki an kuma tsare shi, yakan tsuttsunke su, kazaman ruhohin sukan kora shi cikin jeji.
30Sa'annan Yesu ya tambaye shi, “Yaya sunanka?” Sai ya ba da amsa, “Suna na dubbai.” Ya ce haka ne domin aljanu da yawa sun shiga wannan mutum.
31Aljanun suka yi ta rokon Yesu kada ya ummarce su su shiga cikin rami mai zurfi.
32Akwai babban garken aladu su na kiwo a kan tsauni kusa da wurin. Aljanun suka roki Yesu da ya barsu su shiga cikin aladun, shi kuwa ya yarda masu.
33Aljanun suka bar mutumin suka shiga cikin aladun, sai garken aladun suka gangara kwari suka fada cikin tafkin, suka nutse.
34Lokacin da mutanen da su ke kiwon aladun suka ga abin da ya faru, sai suka gudu! Suka ba da rahoton abin da ya faru ga mutanen cikin gari da na wannan kewayen.
35Don haka, mutanen da suka ji haka suka tafi domin su ga abin da ya faru, suka zo wurin da Yesu yake, suka ga mutumin wanda aljanu suka fita daga cikinsa. Suka ga ya na sanye da tufafi, kuma ya na cikin hankalinsa, sai tsoro ya kama su.
36Mutanen da suka ga abin da ya faru, suka gaya wa wadansu yadda aka warkar da mutumin da aljanu suke iko da shi.

Read Luka 8Luka 8
Compare Luka 8:14-36Luka 8:14-36