Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Luka - Luka 6

Luka 6:41-45

Help us?
Click on verse(s) to share them!
41Don me kake duba dan hakin da ke a idon dan'uwanka, amma ba ka iya ganin gungumen da ke a idonka ba?
42Don me za ka ce wa dan'uwanka, 'Dan'uwa, bari in cire dan hakin da ke a idonka', bayan kai da kanka ba ka iya ganin gungumen da ke a idonka ba? Kai munafuki! Ka fara cire gungumen da ke a idonka, sa'annan za ka gani da kyau yadda zaka cire hakin da ke a idon dan'uwanka.
43Domin babu itace mai kyau da ke haifar rubabbun 'ya'ya, ko rubabben itace da zai haifi kyawawan 'ya'ya.
44Domin ana iya sanin ko wani itace ta wurin 'ya'yan da yake bayarwa. Domin mutane basu kan tsinki 'ya'yan baure a jikin kaya, ko kuwa su dibi inabi daga jikin sarkakkiya.
45Mutumin kirki, daga wadatar zuciyarsa ya kan ba da yaya masu kyau, kuma mugu daga cikin muguwar ajiyar zuciyarsa yake aikata mugunta. Domin daga cikar zuciyarsa ne bakinsa yakan yi magana.

Read Luka 6Luka 6
Compare Luka 6:41-45Luka 6:41-45