Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Luka - Luka 6

Luka 6:3-39

Help us?
Click on verse(s) to share them!
3Yesu ya amsa masu, ya ce, “Ba ku karanta abin da Dauda ya yi a lokacin da yake jin yunwa ba, shi da mutanen da ke tare da shi?
4Ya je cikin gidan Allah, ya dauki gurasar alfarwa ya kuma ci daga ciki, ya kuma ba mazajen da ke tare da shi su ci, ko da shike ya halarta ga Firistoci ne kadai su ci.”
5Sai ya ce masu, “Dan Mutum shi ne Ubangijin asabaci.”
6Ya kasance a wata ranar Asabaci ya shiga cikin majami'a ya kuma koya wa mutane a can. Wani mutum na can wurin wanda hannun damansa ya shanye.
7Marubuta da Farisawa na kallonsa su ga ko zai warkar da wani a ranar Asabaci, domin su samu dalilin zarginsa da yin abin da bai cancanta ba.
8Amma ya san abin da suke tunani, sai ya ce wa mai shanyeyen hannun, “Tashi, ka tsaya a nan tsakiyar jama'a.” Sai mutumin ya tashi ya tsaya a nan.
9Yesu ya ce masu, “Ina tambayar ku, ya halatta a ranar Asabaci a yi nagarta ko mugunta, a ceci rai ko a hallaka shi?
10Sai ya dube su duka, ya kuma ce wa mutumin, “Mika hannunka.” Ya yi haka, sai hannunsa ya koma lafiyayye.
11Amma suka fusata kwarai, suka yi shawara da junansu game da abin da za su yi da Yesu.
12Ya zama a kwanakin nan, ya hawo bisan dutse domin ya yi addu'a. Ya ci gaba dukan dare yana addua'a ga Allah.
13Da safiya ta yi, ya kira almajiransa zuwa wurinsa, ya kuma zabi goma sha biyu daga cikinsu, wadanda ya kira su “Manzanni.”
14Sunayen Manzannin sune Siman (wanda ya kuma kira Bitrus) da dan'uwansa, Andrawus, Yakubu, Yahaya, Filibus, Bartalamawus,
15Matta, Toma, Yakubu dan Halfa, Siman, wanda ake kira Zaloti, Yahuda dan Yakubu,
16da Yahuda dan Iskariyoti, wanda ya zama maci amana.
17Sai Yesu ya gangaro daga dutsen tare da su, suka kuma tsaya a sarari. Almajiransa da yawa na nan a wurin, tare da mutane da yawa daga Yahudiya da Urushalima, da kuma bakin tekun Taya da Sidon.
18Sun zo domin su ji shi, da kuma su sami warkarwa daga dukan cututukansu. Mutane waddan da ke fama da kazaman ruhohi ma sun sami warkarwa.
19Dukan taron jama'ar suna kokarin su taba shi domin ikon warkarwa yana fitowa daga wurinsa, ya kuma warkar da su duka.
20Sai ya dubi almajiransa ya ce, “Masu albarka ne ku matalauta, gama Mulkin Allah naku ne.
21Masu albarka ne ku masu yunwa yanzu, domin za a kosar da ku. Masu albarka ne ku masu kuka a yanzu, domin za ku yi dariya.
22Masu albarka ne ku idan mutane sun ki ku, suka nuna maku wariya suna mai da sunayen ku na mugunta, domin Dan Mutum.
23Za ku yi farin ciki a ranan nan kuna tsalle domin murna, domin hakika za ku samu lada mai girma a sama, domin haka kakannin-kakannin su suka yi wa annabawa.
24Amma kaitonku mawadata! Domin kun rigaya kun samu ta'aziyar ku.
25Kaitonku kosassu a yanzu! Domin za ku ji yunwa nan gaba. Kaitonku masu dariya yanzu! Domin za ku yi makoki kuna kuka nan gaba.
26Kaiton ku idan kowadanne mutane suna yabon ku! Domin haka kakannin-kakanninsu suka yi wa annabawan karya.
27Amma ina ce maku ku masu saurare na, ku kaunaci magabtanku, ku kuma aikata nagarta ga wadanda suke kinku.
28Ku albarkaci masu zaginku, ku kuma yi addu'a ga wadanda suke wulakanta ku.
29Wanda ya mare ku a wannan kunci, ku juya masa dayan. Idan wani ya dauki mayafinka, kada ka hana masa taguwarka.
30Ku bayar ga duk wanda ya roke ku. Idan wani ya dauki wani abu da ke naku, kada ku bidi ya mayar da shi.
31Duk abin da kake so mutane su yi maka, ka yi masu hakan nan.
32Idan ka kaunaci masoyan ka ne kadai, me wannan zai amfane ka? Ko masu zunubi ma na kaunar masoyan su.
33Idan kuna nuna alheri ga wadan da ke maku alheri kadai, menene ladan ku a nan? Ko masu zunubi ma na yin hakan nan.
34Idan kun ba da rancen abubuwa ga mutanen da kuna sa zuciya zasu mayar maku ne kadai, menene ribar ku a nan? Ko masu zunubi suna ba masu zunubi rance, suna kuma sa zuciya a mayar masu dadai gwargwado.
35Amma ku kaunaci magabtan ku, ku kuma nuna masu alheri. Ku basu rance, kada ku sa zuciya a maido maku, kuma sakamakon ku zai zama da girma. Za ku zama yayan Mafifici, domin shi da kansa yana nuna jinkai ga marasa godiya da miyagun mutane.
36Ku zama masu jinkai, domin Ubanku mai jinkai ne.
37Kada ku shari'anta, kuma ba za a shari'anta ku ba. Kada ku kayar, ku ma ba za a kashe ku ba. Ku yafe wa wasu, kuma za a yafe maku.
38Ku bayar ga wasu, ku ma za a ba ku da yawa. Magwaji dankararre, girgizajje har ya cika yana zuba, za su zuba har cinyarku. Domin duk ma'aunin da ku ka yi amfani da shi, da shi za a auna maku.
39Sai ya sake basu wani misali, “Makaho yana iya yi wa makaho jagora? Idan ya yi haka, dukansu biyu za su fada cikin rami, ko ba haka ba?

Read Luka 6Luka 6
Compare Luka 6:3-39Luka 6:3-39