Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Luka - Luka 5

Luka 5:4-23

Help us?
Click on verse(s) to share them!
4Da ya gama magana, ya ce wa Siman, “Zakuda jirgin zuwa wuri mai zurfi sa'annan ka zuba tarunka domin kamu.”
5Siman ya amsa ya ce, “Ubangiji, mun yi aiki dukan dare bamu kama komai ba, amma bisa ga maganarka, zan jefa tarun.”
6Da sun yi haka, suka kama kifaye da yawan gaske, har tarunsu suna yagewa.
7Sai suka roki abokan aikinsu da ke a dayan jirgin su zo su taimake su. Suka zo sun cika jiragen biyu da kifaye, har suka fara nutsewa.
8Amma Siman Bitrus, da ya ga haka, ya russuna a gaban Yesu, yana cewa, “Ka rabu da ni Ubangiji, gama ni mai zunubi ne.”
9Domin ya yi mamaki, da dukan wadanda suke tare da shi, sabili da yawan kifaye da suka kama.
10Wannan ya hada da Yakubu da Yahaya 'ya'yan Zabadi abokan aikin Siman. Sai Yesu ya ce wa Siman, “Kada ka ji tsoro, domin daga yanzu, za ka kama mutane.”
11Da sun kawo jiragensu waje kan kasa, suka bar komai suka kuma bi shi.
12Sa'adda yana daya daga cikin biranen, wani mutum dauke da kuturta yana nan wurin. Da ya ga Yesu, ya fadi bisa fuskarsa kasa yana rokansa, yana cewa, “Ubangji, idan ka yarda, za ka iya tsarkake ni.”
13Yesu ya mika hanunsa ya taba shi, yana cewa, “Na yarda. Ka tsarkaka.” Sai nan da nan, kuturtar ta rabu da shi.
14Ya umarce shi kada ya gaya wa kowa, amma ya ce ma sa, “Tafi ka nuna kanka ga firist sa'annan ka mika hadaya domin tsarkakewarka, kamar yadda Musa ya umarta, a matsayin shaida a garesu.”
15Amma labarinsa ya bazu nesa, taron mutane da yawa kuma suka zo wurinsa domin su ji shi, su kuma samu warkarwa daga cututtukansu.
16Amma ya kan janye zuwa wuraren da babu kowa ya yi addu'a.
17Ya zama daya a cikin kwanakin da yake koyarwa, akwai Farisawa da malaman attaura da ke zaune a wurin wandanda suka zo daga kauyukan da suke kewaye da Galili da Yahudiya da kuma birnin Urushalima. Ikon Ubangiji yana tare da shi domin warkarwa.
18A lokacin nan, wasu mutane suka zo dauke da wani mutum shanyayye a kan tabarma, suka kuma nemi yadda za su shigar da shi ciki, su kwantar da shi a gaban Yesu.
19Ba su iya samun hanyar da za su shigar da shi ba saboda taron, sai suka hau saman gidan, suka saukar da shi daga rufin, a kan tabarman sa, zuwa tsakiyar mutanen, dai dai a gaban Yesu.
20Da ya ga bangaskiyarsu, Yesu ya ce, “Maigida, an gafarta zunubanka.”
21Marubuta da Farisawa suka fara sukar wannan, suna cewa, “Wanene wannan da ke sabo? Wa zai iya gafarta zunubi, idan ba Allah kadai ba?”
22Amma da Yesu ya fahimci abin da suke tunani, sai ya amsa ya ce masu, “Don me kuke sukar wannan a zuciyarku?
23Wanne ne ya fi sauki a ce, 'An yafe zunubanka' ko kuwa a ce, 'Tashi ka yi tafiya?”

Read Luka 5Luka 5
Compare Luka 5:4-23Luka 5:4-23