Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Luka - Luka 4

Luka 4:5-21

Help us?
Click on verse(s) to share them!
5Sai shaidan ya kai shi zuwa wani tudu mai tsawo, ya kuma nuna masa dukan mulkokin duniyan nan a dan lokaci.
6Shaidan ya ce masa, “Zan ba ka iko ka yi mulkin dukan wadannan, da dukan daukakarsu. Zan yi haka domin an ba ni su duka in yi mulkinsu, kuma ina da yanci in ba dukan wanda na ga dama.
7Saboda da haka, idan ka rusuna ka yi mani sujada, dukansu za su zama naka.”
8Amma Yesu ya amsa ya ce masa, “A rubuce yake, 'Dole ne Ubangiji Allahnka za ka yi wa sujada, shi kadai kuma za ka bauta wa.”
9Sai shaidan ya kai Yesu Urushalima, ya tsayadda shi a bisan kololuwar haikali, kuma ya ce masa, “Idan kai Dan Allah ne, ka jefas da kanka kasa daga nan.
10Domin a rubuce yake, 'Zai ba mala'ikunsa umarni su kiyaye ka, su kuma tsare ka,'
11kuma, 'Za su daga ka sama a hannunsu, don kada ka yi tuntube a kan dutse.”
12Yesu ya amsa masa cewa, “An fadi, 'Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.'”
13Da shaidan ya gama yi wa Yesu gwaji, sai ya kyale shi sai wani lokaci.
14Sai Yesu ya koma Galili cike da ikon Ruhu, kuma labarinsa ya bazu cikin dukan wuraren dake wannan yankin.
15Ya yi ta koyarwa a cikin majami'unsu, sai kowa na ta yabon sa.
16Wata rana ya zo Nazarat, birnin da aka rene shi. Kamar yadda ya saba yi, ya shiga cikin majami'a a nan ranar Asabaci, ya kuma tashi tsaye domin ya karanta Nassi.
17An mika masa littafin anabi Ishaya, ya bude littafin ya kuma ga inda an rubuta,
18“Ruhun Ubangiji yana kai na, domin ya shafe ni in yi wa'azin Bishara ga matalauta. Ya aike ni in yi shelar yanci ga daurarru, da kuma budewar idanu ga makafi, in 'yantar da wadanda su ke cikin kunci,
19in kuma yi shelar shekarar tagomashi na Ubangiji.”
20Sai ya rufe littafin, ya mai da shi ga ma'aikacin majami'ar, sai ya zauna. Dukan wadanda suke cikin majami'ar suka zura Idanuwansu a kansa.
21Sai ya fara masu magana, “Yau wannan Nassi ya cika a kunuwanku.”

Read Luka 4Luka 4
Compare Luka 4:5-21Luka 4:5-21