Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Luka - Luka 4

Luka 4:15-41

Help us?
Click on verse(s) to share them!
15Ya yi ta koyarwa a cikin majami'unsu, sai kowa na ta yabon sa.
16Wata rana ya zo Nazarat, birnin da aka rene shi. Kamar yadda ya saba yi, ya shiga cikin majami'a a nan ranar Asabaci, ya kuma tashi tsaye domin ya karanta Nassi.
17An mika masa littafin anabi Ishaya, ya bude littafin ya kuma ga inda an rubuta,
18“Ruhun Ubangiji yana kai na, domin ya shafe ni in yi wa'azin Bishara ga matalauta. Ya aike ni in yi shelar yanci ga daurarru, da kuma budewar idanu ga makafi, in 'yantar da wadanda su ke cikin kunci,
19in kuma yi shelar shekarar tagomashi na Ubangiji.”
20Sai ya rufe littafin, ya mai da shi ga ma'aikacin majami'ar, sai ya zauna. Dukan wadanda suke cikin majami'ar suka zura Idanuwansu a kansa.
21Sai ya fara masu magana, “Yau wannan Nassi ya cika a kunuwanku.”
22Dukan wadanda ke wurin sun shaida abin da ya fadi kuma dukansu sun yi ta mamakin kalmomin alheri da suke fitowa daga bakinsa. Suna cewa, “Wannan ai dan Yusufu ne kawai, ko ba haka ba?”
23Yesu ya ce masu, “Lallai za ku fada mani wannan karin magana, 'Likita, ka warkar da kanka. Duk abin da mun ji wai ka yi a Kafarnahum, ka yi shi a nan garinka ma.'”
24Ya sake cewa, “Hakika na fada maku, annabi baya samun karbuwa a garinsa.
25Amma na gaya maku gaskiya akwai gwauraye da yawa cikin Isra'ila a zamanin Iliya, lokacin da an rufe sammai shekaru uku da rabi babu ruwa, lokacin da anyi gagarumar yunwa a duk fadin kasar.
26Amma ba a aiki Iliya zuwa wurin waninsu ba, sai wurin gwauruwa da ke a Zarifat can kusa da Sidon.
27Akwai kutare da yawa kuma a Isa'ila a zamanin anabi Elisha, amma babu wanda aka warkar sai dai Na'aman mutumin Suriya kadai.
28Dukan mutanen da ke cikin majami'a suka fusata kwarai sa'adda suka ji wadannan zantattuka.
29Suka tashi suka tura shi zuwa wajen birnin, suka kai shi bakin dutsen da aka gina garinsu a kai dominsu jefar da shi kasa.
30Amma ya ratsa tsakaninsu ya yi gabansa.
31Sannan ya gangara zuwa Kafarnahum, wani birni a Galili. Wata Asabaci yana koya wa mutane a cikin majami'a.
32Sun yi mamaki kwarai da koyarwan sa, domin maganarsa na da iko.
33A wannan lokacin akwai wani mutum a cikin majami'a mai kazamin ruhu, sai ya yi kara da babbar murya,
34“Ina ruwan mu da kai, Yesu Banazarat? Ka zo domin ka hallaka mu ne? Na san ko kai wanene! Kai ne Mai Tsarki na Allah!”
35Yesu ya tsauta wa aljanin yana cewa, “Yi shiru ka fita daga cikinsa!” Da aljanin ya jefar da mutumin kasa a tsakiyarsu, ya fita daga cikinsa ba tare da yi masa rauni ba.
36Dukan mutanen suka yi mamaki, kuma suna ta zancen wannan abu a tsakaninsu. Sun ce, “Wanda irin maganganu kenan? Ya umarce kazaman ruhohin da karfi da iko kuma sun fita.”
37Saboda da haka, an fara yada labarinsa zuwa dukan kewayen yankin.
38Sai Yesu ya bar majami'ar ya shiga gidan Siman. A wannan lokacin, surukar Siman tana fama da zazzabi mai zafi, sai suka roke shi dominta.
39Sai ya tsaya a kanta, ya tsautawa zazzabin, kuma ya rabu da ita. Nan take, ta tashi ta fara yi masu hidima.
40Da faduwar rana, mutane suka kawo wa Yesu dukan wadanda suke ciwo da cuttuttuka dabam dabam. Ya dora masu hannuwansa ya warkar da su.
41Aljanu kuma sun fita daga wadasunsu da dama, suna kuka cewa, “Kai ne Dan Allah!” Yesu ya tsauta wa aljannun ya kuma hana su magana, domin sun sani cewa shine Almasihu.

Read Luka 4Luka 4
Compare Luka 4:15-41Luka 4:15-41