Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Luka - Luka 24

Luka 24:44-50

Help us?
Click on verse(s) to share them!
44Sai ya ce masu, “Sa'adda nake tare da ku na gaya maku cewa duka abin da aka rubuta a cikin dokokin Musa da na annabawa da Zabura dole su cika.”
45Sai ya bude hankalinsu, saboda su gane littattafai.
46Ya ce masu, “A rubuce yake, cewa Almasihu za ya sha wuya, zai tashi kuma daga matattu a rana ta uku.
47Ku yi wa'azin tuba da gafarar zunubai a cikin sunansa ga dukan al'ummai, ku fara daga Urushalima.
48Ku shaidu ne ga wadannan abubuwan.
49Duba, ina aiko da alkawarin Ubana a kanku. Amma ku jira a birni, sai an suturta ku da iko daga sama.”
50Sa'annan Yesu ya tafi tare da su har sai da suka kai kusa da Betanya. Sai ya daga hannunsa ya albarkace su.

Read Luka 24Luka 24
Compare Luka 24:44-50Luka 24:44-50