Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Luka - Luka 18

Luka 18:17-27

Help us?
Click on verse(s) to share them!
17Gaskiya ina gaya maku, duk wanda bai karbi mulkin Allah kamar karamin yaro ba, lallai ba zai shige shi ba.”
18Wani shugaban jama'a ya tambaye shi ya ce “Malam managarci, me zan yi in gaji rai Madawwami?”
19Yesu ya ce masa, “Don me ka kira ni managarci? Babu wani managarci sai Allah kadai.
20Ka dai san dokokin - kada ka yi zina, kada ka yi kisankai, kada ka yi sata, kada ka yi shaidar karya, ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka.”
21Sai shugaban ya ce, “Dukan wadannan abubuwa na kiyaye su tun a kuruciya ta.”
22Da Yesu ya ji haka, ya ce masa, “Abu daya ne kadai ya rage maka. Dole ne ka sayar da dukan mallakarka, ka rarraba wa gajiyayyu, za ka kuma sami wadata a sama - sa'annan ka zo ka biyoni.”
23Amma da mai arzikin ya ji wadannan abubuwa, sai yayi bakin ciki kwarai, don shi mai arziki ne sosai.
24Yesu kuwa, da ya ga ransa ya baci, sai ya ce, “Yana da wuya masu dukiya su shiga mulkin Allah!
25Zai zama da sauki rakumi ya shiga kafar allura, da mai arziki ya shiga mulkin Allah.”
26Wadanda suka ji wannan magana suka ce, “Idan hakane wa zai sami ceto kenan?”
27Yesu ya amsa, “Abin da ya fi karfin mutum, mai yiwuwa ne a gun Allah.”

Read Luka 18Luka 18
Compare Luka 18:17-27Luka 18:17-27