Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Luka - Luka 16

Luka 16:14-19

Help us?
Click on verse(s) to share them!
14Da Farisawa da ke da kaunar kudi suka ji dukan wadannan abubuwa, suka yi masa ba'a.
15Sai ya ce masu, “Ku ne masu baratar da kanku a gaban mutane, amma Allah ya san zuciyarku. Abin da mutane suke girmamawa kwarai abin kyama ne a gun Allah.
16Attaura da litattafan annabawa suna nan har zuwan Yahaya. Tun daga lokacin nan ake yin bisharar mulkin Allah, kowa kuma yana kokarin kutsawa zuwa cikinta.
17Duk da haka, zai fi sauki sama da kasa su shude, da ko digo daya na attaura ya shude.
18Duk wanda ya saki matansa ya auri wata ya aikata zina, kuma wanda ma ya auri sakakkiya ya aikata zina.
19Akwai wani mai arziki, mai sa tufafi na alfarma masu tsada yana shagalin sa kowace rana.

Read Luka 16Luka 16
Compare Luka 16:14-19Luka 16:14-19