Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Luka - Luka 15

Luka 15:2-11

Help us?
Click on verse(s) to share them!
2Dukan Farisawa da Marubuta suna ta gunaguni da junansu, cewa, “Wannan mutum yana karbar masu zunubi, har ma tare suke cin abinci.”
3Yesu ya fadi wannan misali, ya ce,
4“Idan waninku yana da tumaki dari, sai dayarsu ta bace, wato ba zai bar tasa'in da taran nan a makiyaya, ya bi sawun wadda ta bata gudan nan har sai ya same shi ba?
5Idan kuwa ya same ta, sai ya dauke ta a kafadarsa yana farin ciki.
6In ya dawo gida, sai ya kira abokansa da makwabta, yace masu, 'Ku taya ni murna don na samo tunkiyata da ta bata.'
7Ina gaya maku, haka kuma za a yi farin ciki a sama, a kan mai zunubi guda da ya tuba, fiye da kan masu adalci tassa'in da tara wadanda ba su bukatar tuba.
8Ko kuwa wacce mace ce, in tana da kudi azurfa guda goma, in ta batar da daya, ba za ta kunna fitila ta share gidan, ta yi ta neman shi har sai ta same shi ba?
9In kuwa ta same shi sai ta tara kawayenta da makwabtanta, ta ce, 'Ku taya ni farin ciki don na sami kudin nan nawa da ya bace.'
10Haka nake gaya maku, abin farin ciki ne ga mala'ikun Allah idan mai zunubi guda ya tuba.”
11Sai Yesu ya ce, “Akwai wani mutum mai 'ya'ya biyu maza,

Read Luka 15Luka 15
Compare Luka 15:2-11Luka 15:2-11