Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Luka - Luka 11

Luka 11:5-11

Help us?
Click on verse(s) to share them!
5Yesu ya ce masu, “Wanene a cikinku idan yana da aboki, za ya je wurinsa da tsakar dare ya ce masa, “Aboki, ka ba ni rancen dunkulen gurasa guda uku,
6da ya ke wani abokina ya iso yanzu daga tafiya, kuma ba ni da abin da zan ba shi ya ci,'
7Sai wanda yake ciki, ya amsa, ya ce, 'Kada ka dame ni. Na riga na rufe kofa ta, kuma ni da yarana mun riga mun kwanta. Ba zan iya tashi in ba ka gurasa ba.'
8Na fada maku, ko da bai tashi ya ba ka gurasar ba, a matsayin abokinsa, ba ka ji kunya ba, ka nace da rokonsa, za ya tashi ya ba ka dukan yawan gurasar da kake bukata.
9Ni kuma ina ce maku, ku roka za a ba ku; ku nema za ku samu; ku kwankwasa za a bude maku.
10Domin dukan wanda yake roko ya na karba; dukan wanda ya ke nema kuma yana samu; kuma wanda yake kwankwasawa, za a bude masa.
11Wanne uba ne a cikinku, idan dansa ya tambaye shi kifi, zai ba shi maciji a maimakon kifi?

Read Luka 11Luka 11
Compare Luka 11:5-11Luka 11:5-11