Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Luka - Luka 11

Luka 11:24-36

Help us?
Click on verse(s) to share them!
24Idan kazamin ruhu ya fita daga cikin mutum, ya kan bi ta wurin busassun wurare yana neman wurin da zai huta. Idan bai samu ba sai ya ce, 'Bari in koma gidana inda na baro.
25Sa'adda ya dawo, ya tarar an share gidan, an kuma gyara shi tsaf.
26Sai ya je ya dauko wadansu aljanu guda bakwai wadanda su ka fi shi mugunta, su zo su zauna a wurin. Sai karshen mutumin nan ya fi farkonsa muni.”
27Ya zama, lokacin da ya ke fadin wadannan abubuwa, wata mace ta tada muryarta a cikin taron mutanen ta ce da shi, “Mai albarka ne cikin da ya haife ka, da maman da ka sha.”
28Sai shi kuma ya ce, “Masu albarka ne wadanda suke jin maganar Allah suke yin biyayya da ita.”
29Lokacin da mutane suke kara taruwa, sai ya fara cewa, “Wannan tsara, muguwar tsara ce. Ta na neman alama, Ko da yake ba wata alamar da za a bata sai irin ta Yunusa.
30Domin kamar yadda Yunusa ya zama alama ga mutanen Neneba, haka kuma Dan Mutum za ya zama alama ga wannan tsara.
31Sarauniyar Kudu, za ta tsaya ta yi shari'a da mutanen wannan tsara, kuma za ta kashe su, gama ta zo daga wuri mai nisa domin ta saurari hikimar Sulaimanu. Kuma ga wani wanda ya fi Sulaimanu a nan.
32Mutanen Neneba, za su tsaya shari'a da matanen wannan tsara, kuma za su kashe su. Gama sun ji wa'azin Yunusa sun tuba. Kuma ga wani wanda ya fi Yunusa a nan.
33Ba wanda zai kunna fitila ya boye ta, ko kuwa ya sa ta a karkashin kasko, amma zai sa ta a mazaunin ta domin dukan wanda ya shiga dakin ya ga haske.
34Idon ku shine fitilar jikinku. Idan idonku yana gani sosai, jikinku zai cika da haske. Amma idan idonku ba ya gani sosai, jikinku zai cika da duhu.
35Ku yi hankali fa, domin kada hasken da ya ke wurinku ya zama duhu.
36Idan dukan jikinku yana cike da haske, babu duhu ko kadan, to sai dukan jikinku ya zama kamar fitilar da take bada haskenta a bisanku.”

Read Luka 11Luka 11
Compare Luka 11:24-36Luka 11:24-36