Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Ayyukan Manzanni - Ayyukan Manzanni 9

Ayyukan Manzanni 9:9-18

Help us?
Click on verse(s) to share them!
9Har kwana uku ba ya kallo, kuma ba ya ci balle sha.
10Akwai wani almajiri a Dimashku mai suna Hananiya; sai Ubangiji ya yi magana da shi cikin wahayi, ya ce, “Hananiya.” Sai ya ce, “Duba, gani nan Ubangiji.”
11Ubangiji ya ce masa, “Tashi, ka tafi titin da ake kira Mikakke, kuma a gidan wani mai suna Yahuza ka tambaya mutum daga Tarsus mai suna Shawulu; gama yana addu'a;
12kuma ya gani cikin wahayi mutum mai suna Hananiya na shigowa kuma ya daura masa hannu, domin idanunsa su bude.”
13Amma Hananiya ya amsa, “Ubangiji, na ji labari daga wurin mutane da yawa game da mutumin nan, da irin muguntar da ya aikata ga tsarkakan mutanenka da ke Urushalima.
14An bashi izini daga babban firist domin ya kama dukan wanda ke kira bisa sunanka.”
15Amma Ubangiji ya ce masa, “Jeka, gama shi zababben kayan aiki na ne, wanda zai yada sunana ga al'ummai da sarakuna da 'ya'yan Isra'ila;
16Domin zan nuna masa irin wahalar da zai sha sabo da sunana.”
17Sai Hananiya ya tafi, ya shiga gidan. Ya dora masa hannu a kai, ya ce, “Dan'uwa Shawulu, Ubangiji Yesu, wanda ya bayyana a gareka a hanya sa'adda kake zuwa, ya aiko ni domin ka sami ganin gari ka kuma cika da Ruhu Mai Tsarki.”
18Nan take wani abu kamar bawo ya fado daga idanun Shawulu, kuma ya sami ganin gari; ya tashi aka yi masa baftisma;

Read Ayyukan Manzanni 9Ayyukan Manzanni 9
Compare Ayyukan Manzanni 9:9-18Ayyukan Manzanni 9:9-18