Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Ayyukan Manzanni - Ayyukan Manzanni 9

Ayyukan Manzanni 9:19-34

Help us?
Click on verse(s) to share them!
19kuma ya ci abinci sai aka karfafa shi. Ya zauna tare da almajirai a Dimashku kwanaki da yawa.
20Nan take ya fara shellar Yesu cikin haikali, yana cewa shine dan Allah.
21Dukan wadanda suka saurare shi suka yi mamaki suka ce “Ba wannan mutumin ne yake hallaka mutanen Urushalima da ke kira bisa ga wannan suna ba? Ya kuma zo nan domin ya ba da su a daure ga manyan firistoci.”
22Amma Shawulu kuwa ya sami iko sosai, kuma yana haddasa damuwa tare da rinjaya tsakanin Yahudawan dake zama a Dimashku ta wurin tabbatar da Yesu shine Almasihu.
23Bayan kwanaki da yawa, sai Yahudawan suka yi shiri domin su kashe shi.
24Amma shirin su ya zama sananne ga Shawulu. Suna fakkon sa ta wurin tsaron kofar birnin dare da rana domin su kashe shi.
25Amma da tsakar dare almajiransa suka daukeshi a kwando, suka zurara shi ta katanga.
26Sa'adda ya zo Urushalima, Shawulu ya yi niyyar hada kai da almajirai, amma dukansu suna tsoronsa, domin ba su yarda cewa shima ya zama almajiri ba.
27Amma Barnaba ya dauke shi ya kawo shi wurin manzannin. Ya kuwa gaya musu yadda Shawulu ya sadu da Ubangiji a hanya, har Ubangiji ya yi magana da shi, kuma yadda Shawulu ya yi wa'azi cikin sunan Yesu gabagadi a Dimashku.
28Ya sadu da su lokacin shigar su da fitar su a Urushalima. Ya yi wa'azi gabagadi cikin sunan Ubangiji Yesu
29kuma yana muhawara da Yahudawan Helenanci; amma sun ci gaba da kokarin kashe shi.
30Da 'yan'uwa suka gane haka, sai suka kawo shi Kaisariya, suka kuwa tura shi zuwa Tarsus.
31Sa'annan iklisiya dake dukan kasar Yahudiya, Galili da kuma Samariya suka sami salama da kuma ginuwa; suka kuwa ci gaba da tafiya cikin tsoron Ubangiji, da kuma ta'aziyar Ruhu Mai Tsarki, iklisiyar kuwa ta karu da yawan mutane.
32Har ta kai, yayin da Bitrus ya zaga dukan yankin kasar, ya dawo wurin masu bi dake zama a garin Lidda.
33A can kuwa ya sami wani mutum mai suna Iniyasu, wanda yake shanyayye ne, yana kwance har tsawon shekara takwas a kan gado.
34Bitrus ya ce masa, “Iniyasu, Yesu Almasihu ya warkar da kai. Tashi ka nade shimfidarka.” Nan take sai ya mike.

Read Ayyukan Manzanni 9Ayyukan Manzanni 9
Compare Ayyukan Manzanni 9:19-34Ayyukan Manzanni 9:19-34