Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Ayyukan Manzanni - Ayyukan Manzanni 5

Ayyukan Manzanni 5:18-33

Help us?
Click on verse(s) to share them!
18suka kama manzannin suka kuma jefasu a kurkuku.
19A cikin dare sai mala'ikan Ubangiji ya bude kofofin kurkukun ya kuma fito da su waje, ya ce,
20“Kuje ku tsaya a gaban haikali ku kuma gaya wa mutane maganar wannan rai.”
21Sa'adda suka ji haka, sai suka tafi haikalin da wayewar gari suka yi koyarwa. Amma babban firist da jama'arsa suka zo suka kuma kira taro da kuma dukan yan majalisa, da dattawan jama'ar Isra'ilawa suka fito suka kuma ba da umarni, a fito masu da manzannin.
22Amma ma'aikatan da suka je kurkukun basu sami kowa, a kurkukunba, sai suka dawo suka ba da rahoto,
23Su ka ce kurkukun a rufe gam da masu gadi suna nan a tsaye a bakin kofar amma da muka shiga, bamu sami kowa a ciki ba.
24Yanzu sa'adda shugaban haikalin da manyan firistoci suka ji wadannan kalamai, sai suka rikice sosai game da su, suka ce yanzu me wannan zai haifar.
25Sai wani ya zo ya ce masu, “Wadannan mutanen da kuka jefa a kurkuku suna can a cikin haikali suna koyar da jama'a.”
26Sai shugaban haikalin ya je da ma'aikatansa suka kawosu, ba tare da tashin hankali ba, domin gudun kada jama'a su jejjefesu.
27Da suka kawo su, sai suka gabatar da su gaban majalisa, babban firist kuwa ya tuhume su,
28cewa “Ba mun yi maku kashedi da karfi kada ku yi koyarwa cikin wannan sunan ba? Amma ga shi duk kun cika Urushalima da koyarwarku, kuna kuma neman kusa jinin mutumin nan ya sauko kanmu.”
29Amma Bitrus da manzannin suka amsa suka ce, “Dole mu yi wa Allah biyayya ba mutane ba.
30Allah na ubanenmu ya ta da Yesu, wanda kuka kashe, ta wurin rateye shi a bisa itace,
31Allah kuwa ya daukaka shi a hannun damarsa, domin ya zama sarki da kuma mai ceto, ya ba Isra'ila tuba da gafarar zunubai.
32Mu kuwa shaidu ne ga wadannan al'amura, haka ma Ruhu Mai Tarki, wanda Allah ya bayar ga dukan wadanda suka yi biyayya a gareshi.”
33Da yan majalisa suka ji haka sai suka fusata kwarai da gaske, har suka nemi su kashe manzannin.

Read Ayyukan Manzanni 5Ayyukan Manzanni 5
Compare Ayyukan Manzanni 5:18-33Ayyukan Manzanni 5:18-33